Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-25 18:56:19    
'Ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu masu launukan ja da shuni da kuma shudi suna iya ba da taimako wajen shawo kan sankara

cri

Manazartan da ke karkashin jagorancin Monica Giusti, kwararriya a fannin abincin tsire-tsire na jami'ar jihar Ohio ta kasar Amurka sun tace sinadarin anthocyanin daga 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu masu launukan ja wur da shudi da kuma shuni, da kuma kara su cikin bututun gwaji da ke da kwayoyin sankarar hanji.

Kuma lokacin da kungiyar nazari ke yin kidaya kan cewa, za a bukaci sinadaran anthocyanin nawa wajen rage saurin karuwar kwayoyin sankara har kashi 50 cikin dari, sun gano cewa, sinadarin da suka samu daga masara mai launin shuni ya fi ba da amfani a wannan fanni, kuma lemo shi ma yana da amfani. Amma game da karamin radishi, idan ana son samun sakamako iri daya, to za a bukace su da yawansu ya kai ninki sau 9 bisa na abubuwa biyu da muka ambata a baya.

A cikin gwaji na biyu da aka yi, manazarta sun bai wa wata karamar bera da ta kamu da sankarar hanji abincin da ke kunshe da sinadarin anthocyanin da aka samu daga lemo domin kwatanta da wata karamar bera daban da ba ta ci abincin da ke kunshe da sinadarin ba. Daga baya kuma an gano cewa, girman tsiron sankarar hanji da ke cikin jikin karamar bera da ta ci abincin da ke kunshe da sinadarin ya ragu da kashi 60 zuwa kashi 70 bisa dari.

Madam Giusti, ta bayyana cewa, dukkan 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu da ke kunshe da sinadarin anthocyanin da yawa suna iya ba da taimako wajen hana kwayoyin sankarar hanji.


1 2