Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-25 18:56:19    
'Ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu masu launukan ja da shuni da kuma shudi suna iya ba da taimako wajen shawo kan sankara

cri

Bisa wani nazarin da masu ilmin kimiyya na kasar Amurka suka yi, an gano cewa, kara yawan sinadaran launuka na zahiri na ja da shuni da kuma shudi da ke cikin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu zai iya ba da taimako wajen shawo kan sankara.

Wadannan sinadaran launi na zahiri da aka samu a cikin gauta da jan kebiji da kuma lemo iri na Turai suna iya hana girman kwayoyin sankara, haka kuma suna iya kisan kwayoyin sankara a wasu lokuta yayin da yake kare kyawawan kwayoyi.

Bisa labarin da jaridar Guardian ta kasar Birtanya ta bayar, an ce, an bayar da wannan sakamakon nazari ne a gun taron shekara-shekara da kungiyar ilmin magunguna ta kasar Amurka ta kira a birnin Boston na kasar Amurka.

Kuma an labarta cewa, a cikin nazarin, an hada hanyar gudanar da bincike ga kwayoyin sankara na dan Adam a cikin dakin gwaje-gwaje da gwajin dabbobi tare domin duba ko abincin da ke kunshe da dimbin sinadarin launi na zahiri zai ba da tasiri ga bunkasuwar cutar sankara ta dabbobi ko a'a.

Daga baya kuma an gano cewa, abincin da ke kunshe da sinadarin launi na zahiri da yawa ya ba da taimako a bayyane wajen rage saurin girman kwayoyin sankara. A cikin gwajin da aka yi, masara mai launin shuni ta hana girman kwayoyin sankarar hanji, da kuma kashe irin wadannan kwayoyin sankara da yawansu ya kai kashi 20 cikin dari. Amma abincin da ke kunshe da sinadarin launi na zahiri kadan, kamar karamin radishi sun rage saurin karuwar kwayoyin sankarar hanji har kashi 50 zuwa kashi 80 cikin dari.

1 2