Yanzu aikin fama da bala'in girgizar kasa ya riga ya shiga wani sabon mataki, wato sake raya yankuna masu fama da bala'in. Sabo da haka, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta tsara sabbin muhimman ayyukan da za ta yi domin wannan sabon nauyin da ke bisa wuyanta. Mr. Hui ya ce, gwamnatin tsakiyar kasar Sin za ta kebe kudin Sin yuan biliyan 70 domin kafa asusun sake raya yankuna masu fama da bala'in. Kuma za a yi amfani da kudin Sin yuan biliyan 40 daga cikinsu domin gina gidaje domin wadanda suke shan wahalar bala'in. Mr. Hui ya ce, "Lokacin da muke sake raya yankuna masu fama da bala'in, dole ne mun dauki matakan da suke dacewa da halin da ake ciki a yankuna da tsimin yankuna da kiyaye gonaki ta hanyoyin kimiyya da tabbatar da zaman karko. A waje daya kuma, za mu ci gaba da yin namijin kokarinmu wajen ceton wadanda suka jikkata cikin bala'in domin raguwar yawan mutanen da suka mutu ko suka zama nakasassu. Bugu da kari kuma, za a yi kokarin samar da guraban aikin yi ga wadanda suke fama da bala'in a lokacin da ake sake raya yankuna masu fama da bala'in. Kuma a yi kokarin kara yawan kudin shiga da za su samu."
A waje daya kuma, Hui Liangyu ya jaddada cewa, sake raya yankuna masu fama da bala'in wani nauyi ne da ke bisa wuyanmu cikin gaggawa, kuma za a sauke shi cikin dogon lokaci mai zuwa. Ya ce, "A lokacin da ake tsara babban shirin da shirye-shirye na fannoni daban daban, dole ne a dogara da halin da ake ciki a yankuna daban daban, kuma a tsara su bisa ilmin kimiyya domin tsara shirye-shiryen da suke da inganci mai kyau. Kuma dole ne a tsaya kan matsayin mai da dan Adam a gaban kome. Za a sake samar da ayyukan yau da kullum da na jama'a da suke da nasaba da zaman rayuwar jama'a da farko." 1 2
|