Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-24 18:32:33    
Gwamnatin kasar Sin ta mai da dan Adam a gaban kome lokacin da take sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa a Sichuan

cri

A ran 24 ga wata, Mr. Hui Liangyu, mataimakin babban mai ba da umurnin fama da bala'in girgizar kasa da ceton mutane na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya wakilci gwamnatin kasar Sin ya bayar da wani jawabi kan yadda aka yi fama da bala'in girgizar kasa da ceton mutane da kuma yadda ake sake raya yankuna masu fama da bala'in da ya auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ga zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin, wato hukumar koli ta ikon mulkin kasar.

Bayan aukuwar bala'in girgizar kasa na Wenchuan a ran 12 ga watan Mayu, a lokacin da take fama da shi, gwamnatin kasar Sin ta sa aikin ceton mutane masu shan wahalar bala'in a gaban kome. Idan ya kasance da dama, sai ta yi namijin kokarinta na ceton mutane, ba ta kasa kokarinta ko kadan ba. Bisa kididdigar da aka yi, yawan mutanen da aka cece su daga kangon gine-gine ya kai dubu 84 da 17.

A cikin jawabinsa, Hui Liangyu, mataimakin firayin ministan gwamnatin kasar Sin wanda ya yi shekaru da dama yake kula da aikin fama da bala'u daga indallahi ya ce, "A karo na farko ne muka tsai da kudurin yin zaman makoki har kwanaki 3 domin fararun hula wadanda suka rasu a cikin bala'in, kuma a karo na farko ne Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ta sauka tutarta domin fararun hula da suka rasu a cikin bala'i daga indallahi. Kuma a karo na farko ne muka yarda da kungiyoyin jin kai na kasashen waje da su shiga yankuna masu fama da bala'in kai tsaye domin ceton mutane wadanda aka binne su a cikin kangon gine-gine, amma ba su rasu ba. A waje daya kuma, a karo na farko ne muka yi amfani da jiragen kasa da motocin daukar marasa lafiya da jiragen sama na kaya da jiragen sama masu saukar ungulu domin sufurin mutanen da suka jikkata da kayayyakin jin kai musamman. Bugu da kari kuma, a karo na farko ne muka yada labaru game da ayyukan fama da bala'in a duk kwana har na tsawon kwanaki. Sauran kasashen Duniya sun mai da hankulansu sosai kan wannan matakin da muka dauka."

1 2