Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-24 17:52:05    
Yin wasa da rairayi a wurin samun karar rairaiyi na Xiangshawan

cri

A cikin wannan hamada mai fadi, akwai wani ayarin rakuma. Mutane sun iya ratsa hamadar kan rakuma. Yin yawo a hamada kan rakuma tare da amon kararawa mai dadin ji da aka sanya a wuyan rakuman da kuma nisantar da kansu daga zaman rayuwar birane sun sanya mutane su kwantar da hankulansu. Bai Jiaona, wata ma'aikaciyar da ke aiki a wurin yawon shakatawa na hamadar Xiangshawan, ta gaya mana cewa,'Mutane da yawa sun fi nuna sha'awa kan hawan rakuma. A da da yawa daga cikinsu ba su taba hawan rakuma ba. Masu yawon shakatawa sun ji mamaki sosai a lokacin da suke kan rakuma. Haka kuma, sun ji sha'awa kwarai a lokacin da suke kan rakuman, rakuman suna tafiya sannu sannu.'

Wurin yawon shakatawa na hamadar Xiangshawan na cikin birnin Erdos na jihar Mongolia ta Gida. Wannan birni, wuri ne da 'yan kabilu da yawa suke zama tare, kuma 'yan kabilar Mongolia sun sami rinjaye. A birnin, mutane sun iya more idanunsu da ni'imtattun wurare a hamada, haka kuma, sun iya kara saninsu kan al'adun kabilar Mongolia a ko ina. Ga shi, 'yan mata da matasa maza na kungiyar fasaha ta hamadar Xiangshawan sun nuna mana wasan kwaikwayo kan bikin aure na Erdos na kabilar Mongolia. Mr. Li ya yi mana bayani da cewa,'Wasan kwaikwayo kan bikin aure na Erdos na da muhimmanci sosai a al'adun kabilar Mongolia a Erdos. Ya hada da yawancin muhimman wakoki da raye-raye na kabilar Mongolia. Ana wake-wake da raye-raye domin nuna motsin rai . Duk wasan kwaikwayon cike yake da murna. Bayan da masu yawon shakatawa suka kalli wannan wasan kwaikwayo, su kan ji farin ciki sosai, an daukaka su kwarai.'

Baya ga wasan kwaikwayo kan bikin aure na Erdos, masu yawon shakatawa sun iya sayen abubuwan fasaha masu halayen musamman na kabilar Mongolia iri daban daban da aka kera da hannu, kuma ake sayar da su a shaguna a wurin yawon shakatawa na hamadar Xiangshawa. Kayayyakin zinariya da na azurfa da na tagulla masu kyan gani da tufafi irin na kabilar Mongolia masu launuka daban daban da kuma wukake masu halayen musamman na kabilar Mongolia su ne suke fi jawo sha'awar masu yawon shakatawa.


1 2