Yau ma za mu kai ziyara ga wurin yawon shakatawa na wurin samun karar rairayi na Xiangshawan, da ke jihar Mongolia ta Gida mai cin gashin kanta a arewacin kasar Sin.
Ma iya cewa, hamadar Xiangshawan, abu ne mai ban mamaki a duniyarmu. Halin musamman nasa shi ne in rairayi ya bushe sosai, kuma ya sauka daga tudun rairayi, ana iya sauraren amon rairayin, sai ka ce wani jirgin sama na tafiya a sararin sama, har ma a duk kwari ana iya sauraren karar rairayi kamar yadda jirgin saman yake yi. Sa'an nan kuma, akwai wata almara mai ban sha'awa da ke bazuwa a wurin. An ce, a can can can da, wani aljanna ba ta mai da hankali sosai ba, ba ta tsuke bakin jakarsa mai dauke da rairayi ba. Da zarar rairayin ya fada daga jakar, sai ya zama hamada. Aljannar ta yi da-na-sani sosai, shi ya sa ya kebe wani wurin da ke gabashin hamadar da ya zama karamar hamada, ya kuma gayyaci wani aljanna daban da ya yi mulkin wannan karamar hamada, ya kuma kira ta hamadar Xiangshawan. Tun daga nan ne aka iya sauraren amon rairayi a wurin ba tare da katsewa ba. Ko da wannan almara na da ban sha'awa, amma ba a iya gano dalilin da ya haddasa amon rairayin ba. Li Mingke, wani kwararre ne mai nazarin hamadar Xiangshawan ya gaya mana cewa,'Bayan da masu nazarin kimiyya suka sha yin bincike da tabbata, yanzu mun gano bayanai 2 kan dalilin haddasa amon rairayin. Da farko dai, rairayin sun a karar da juna sosai, har ma sun samar da amo a lokaci daya. Wasu na ganin cewa, iska na ta buga, har ma rairayin sun zama wadanda girmansu ya yi kusan iri daya, shi ya sa in suna karar da juna sosai, sun iya motsawa a lokaci daya. Duk da haka, ba a tabbatar da wadannan bayanai a karshe ba tukuna, shi ya sa ya zuwa yanzu, ba a san dalilin da ya haddasa amon rairayin ba tukuna.'
Irin wannan abun al'ajabi ya kawo wa hamadar Xiangshawan abun ban mamaki. Mutane da yawa da suka yi bulaguro a hamadar Xiangshawan sun sauka daga tudun rairayi domin sauraren amon rairayi da kunnensu. Su kan sanya safofin musamman a kafafunsu, sun hau tudun rairayin, daga baya, sun zauna ko kuma sun kwanta, sun yi amfani da hannunsu, sun sauka daga tudun. A daidai wannan lokaci, su kan ji amon rairayin, wani lokaci, sai ka ce, kwadi sun yi kuka tare, wani lokaci kuma, sai ka ce, an yi mahaukaciyar guguwa. Ga shi masu yawon shakatawa 2 sun sauka daga tudun rairayin dazun nan, a wani bangare, sauka daga tudun rairayi na matukar sha'awa, a wani daban kuma, rairayin da ke iya samar da amo na da ban mamaki a gare su. Sun ce,'Wannan ne karo na farko da na kawo hamadar Xiangshawan ziyara, ina jin matukar farin ciki. Sauka daga tudun rairayin ya fi ban sha'awa. Sauka daga tudu mai hadarin hakan na da matukar sha'awa, sai ka ce, ina tafiya a sararin sama.'
'A ganina, tukin mota a hamadar Xiangshanwa na da sha'awa ainun, a lokacin da nake hawanta, zuciyata ta bugu da karfi. Ina jin farin ciki sosai.'
1 2
|