Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-23 19:42:10    
Masana'antun kasar Sin na kokarin samar da tantuna ga wuraren lardin Sichuan da bala'in girgizar kasa ya gabalaita

cri

Kamfanin Silver Green wata masana'antar musamman ta samar da tantuna. Bayan aukuwar mummunar girgizar kasa a yankin Wenchuan na lardin Sichuan, kamfanin ya sami takardar odar tantuna dubu 36 daga ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar. Da yake tantunan da aka yi odarsu sun yi yawa, sai nan da nan dukan ma'aikatan kamfanin sun fara yin iyakacin kokari wajen dinken tantuna dare da rana. Da malam Tang Ye, shugaban kwamitin gudanarwa na kamfanin ya tabo magana a kan wannan, sai ya ce, " na farko, mun ba da kwarin gwiwa ga ma'aikata cikin gaggawa. Na biyu, mun daina dinkin tantunan da za mu sayar da su zuwa kasashen ketara, sa'an nan mun yi amfani da dukan na'urorinmu wajen yin tantunan da za a samar da su domin wuraren da bala'in girgizar kasa ya shafa. Na uku, mun sayi danyun kayayyaki cikin gaggawa, a sa'i daya kuma mun kara dinkin tantuna ba tare da wani jinkiri ba."

Malam Tang Ye ya kara da cewa, ko da yake yin haka zai kawo hasara ga kamfaninsa a wasu fannoni, amma a lokacin da ake fuskantar mummunan bala'i, dukan jama'ar kasar Sin za su yi takama da ba da taimakonsu ga wuraren da bala'in ya galabaita.

Bayan aukuwar bala'in girgizar kasar, babban kamfanin yin kayayyakin shakatawa mai suna Top Leisure na birnin Huzhou shi ma ya sami takardar odar tantuna dubu 50 da ake bukata a cikin wata guda. Bayan haka kamfanin ya shirya kwararru ma'aikata sama da dubu 4 da su dinke tantuna ba dare ba rana. Malam Zuo Zongqin, daya daga cikin kwararrun wanda ya fito daga lardin Sichuan ya bayyana cewa, "tantuna su ne abubuwan da ake fama da karancinsu a wuraren da bala'in ya shafa. Sabo da haka kamata ya yi, mu yi iyakacin kokari wajen kara samar da tantuna, ta yadda 'yan'uwan wurin da aka haife ni za su sami wurin kwana tun da wuri."

An ruwaito cewa, ba ma kawai babban kamfanin Silver Green zai kammala aikin samar da tantuna da yawansu ya kai dubu 36 a cikin wata guda ba, har ma zai iya samar da karin tantunan da yawansu zai wuce dubu 10. An yi hasashe cewa, babban kamfanin Top Leisure ma zai kammala aikin samar da tantuna dubu 50 cikin lokacin, kuma zai iya samar da karin tantuna a kalla dubu 30. (Halilu)


1 2