A ran 12 ga watan Mayu da ya wuce, an yi mummunar girgizar kasa a yankin Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin, sakamakon haka gidaje masu dimbin yawa sun ruguje. A lokacin da ake farfado da yankin, ana bukatar tantuna masu dimbin yawa don tsugunar da mutanen da bala'in ya shafa. Sabo da haka gwamnatin kasar Sin tana kokari sosai wajen shirya harkokin samar da su, kuma ta tsara shirin samar da tantunan da yawansu ya kai dubu 900 domin yankin a cikin wata daya.
Yanzu, bi da bi masana'antun yin tantuna na kasar Sin sun daidaita shirin aikinsu, sun shirya ma'aikatan da su kara kokari wajen yin tantuna don samar da su ga lardin Sichuan da girgizar kasa ta shafa. A ran 22 ga watan jiya, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi rangadin aiki a birnin Huzhou na lardin Zhejiang musamman don yin bincike a kan yadda ake yin tantuna. Jama'a masu sauraro, yanzu bari mu zagaya da ku cikin masana'antun yin tantuna na birnin Huzhou.
A wuraren aiki na babban kamfanin yin kayayyakin yawon shakatawa da ake kira Silver Green, ma'aikata suna nuna kwazo da himma wajen dinke tantuna da kekunan dinki, wasu suna nadawa, wasu kuma suna dauka, kai dukan ma'aikata suna aikin wurjanjan don samar da tantuna ga lardin Sichuan na kasar Sin da bala'in girgizar kasa ya galabaita. Mai dinki Zeng Qu ta bayyana cewa, "bauta wa jama'ar da bala'in girgizar kasa ya shafa, aiki ne da ya kamata mu yi. Mun samar da wadannan tantuna don taimake su wajen maganin iska da ruwan sama, ta yadda za su ji dadin zamansu."
1 2
|