Malam Haijia Tola, babban sakataren majalisar nazarin al'adun kabilar Tatar ta birnin Yili ya ce, a cikin goyon baya da manufofin kabilu ta gwamnatin tsakiya ta yi, musamman ma manufofin ba da taimako ga kabilu masu mutane kadan domin samun bunkasuwa, tun daga shekarar 2002, majalisar nazarin ta kafa kos na koyon yaren harshen kabilar Tatar. Ya ce, "Mun shirya kwasa kwasai a lokacin hutu, haka kuma ba za a kawo tasiri ga yara wajen shiga makaranta na yau da kullum ba. Mutanen da suka shiga kwasa kwasai suna da yawa, wadanda suke kunshe da yara da tsoffafi."
Kokarin da kabilar Tatar ta Yili ta yi a kan yada al'adun harshenta ya samu sakamako mai kyau, bayan haka kuma, M.D.D. ta mai da bikin "Saban", wato bikin gargajiya na kabilar Tatar, a matsayin muhimmin bikin gargajiya. 1 2 3
|