Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-19 10:39:15    
'Yan kabilar Tatar da ke mayar da hankali kan aikin ba da ilmi, musamman ma aikin ba da ilmi na gida

cri

Malam Iliyar ya yi aure ne a lokacin da yawan shekarunsa ya kai 50 da haihuwa, matarsa ita ce wata 'yar kabilar Ozbek ce, suna da 'ya daya, da 'da daya. Matarsa kuma ta koyi harshen Tatar, domin ba da ilmi ga yaransu da sauki. Malam Iliyar ya bukaci duk 'yan iyalinsa su yi magana da harshen Tatar a gidansu.

Ili Feila, 'yar malam Iliyar tana koyo a sashen gudanar da sha'anin yawon shakatawa na jami'ar Xinjiang, ita kwararriya ce wajen koyon harsuna, tana iya harsuna iri 6, kamar su: harshen Tatar, da Sinnanci, da harsunan Uygur, da Kazakh, da Rasha, da kuma Turanci, yanzu tana koyon harshen Japan. Ili Feila ta ce, dalilin da ya sa take koyon harsuna da yawa shi ne, tana fatan zama wata ja-gorar yawon shakatawa ta duniya. A lokacin da take Magana kan yadda take koyon harshen Tatar, ta ce, "Duk makwabtanmu su ne 'yan kabilar Uygur ne, babu wadanda ke iya magana da harshen Tatar, a cikin gidanmu, babana da mamata sun bukaci mu yi magana da harshen Tatar. Idan na yi magana da ubana da harshen Uygur, ba zai kula ni ba."

Malam Ili Yar ya gaya wa manema labaru na rediyonmu cewa, akwai wata maganar da ka yi, domin bayyana dangantakar da ke tsakanin 'yan kabilar Tatar da aikin bad a ilmi, wato "Wurarren da 'yan kabilar Tatar ke zama, wurarre ne da ke da makarantu". Idan babu makarantu, to, 'yan kabilar Tatar za su kafa wani. Kullum kabilar Tatar tana mai da maza da mata a matsayin daidai wa daida a fannin ba da ilmi. Mr. Habdulah Dubin, wani shahararren mai ba da ilmi ne na kabilar Tatar ya taba ganin cewa, idan wata uwa jahila ce, to, ba za ta iya horar da kwararru ba, sabo da haka, tilas ne uwa ta koyi ilmi da farko. A shekarar 1915, an kafa makarantar mata ta kabilar Tatar ta farko, makarantar ta karbi matan kabilun Tatar, da Uygur, da kuma Kazakh, ita ce kuma makarantar mata ta farko da aka kafa a jihar Xinjiang.


1 2 3