Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-18 14:19:19    
Mutanen Tibet sun yi zantuka kan abubuwan da suka faru a da a jihar Tibet

cri

Mr Tashi Wangdu ya ci gaba da cewa, a shekarar bara da muka sake shiga wannan gandun noma don daukar sinima, mun taba ganin fatu da sauran kayayyaki masu daraja sosai da aka shigo da su daga kasashen waje. Mai gandun noma ya kan tafi zuwa kasashen waje tare da mutanen iyalansa. Matarsa da sauran matan danginsu suna amfani da kayayyakin ado da ke da suna sosai a Turai, amma a wurin da ke waje da gandun noman, bayi manoma da yawansu ya wuce kashi 95 cikin dari bisa yawan mutanen Tibet suna fama da talauci a bakin mutuwa.

Kafin yin kwaskwarimar dimokuradiya a Tibet a shekarar 1959, Tibet ta kasance cikin matakin aiwatar da tsarin gargajiya na bautawa iyayengijin bayi manoma . babban jami'in cibiyar nazarin Tibet ta kasar Sin Mr Lhagpa Phuntshogs ya bayyana cewa, a da, dokar Tibet ta tsai da cewa, an raba mutane bisa matakai 3 da kananan matakai 9, wato a kowane mataki, an kasa shi cikin kananan matakai uku, wato dukkan matakai uku sun zama matakai 9 ke nan, an kasa mutane cikin matakai 9, sai rayukansu na da banbancin daraja bisa matakai 9, in an kashe wani mutun da ke bisa matakin sama, sai darajar ransa ya kai farashin zinariya,amma wanda ke bisa matsayin kasa, darajar ransa ya kai farashin igiyar ciyawa kawai. A wancan lokaci iyayengijin bayi manoma da bayi manoma ba su yi zaman daidai wa daida ba.Wani mataimakin shugaban jami'ar kabilu ta tsakiya ta kasar Sin wanda aka haife shi a shekarar 1955, wato kafin kwaskwarimar dimokuradiya da aka yi ya bayyana cewa, bayan an yi kwaskwarimar dimokuradiya a Tibet, 'ya'yan bayi manoma sun sami damar shiga makarantu, har ma wasu sun shiga jami'o'I, ya ce, shiga makaranta ya canja zaman rayuwarsa, yaran da ke zama a zamanin yau sun fi mu samun damar karatu. Ya bayyana cewa, a da, babu makaranta ko daya a Tibet, amma yanzu an samu makarantun firamare da na sakandare har da jami'o'I a Tibet. Yanzu, 'yan makarantun Tibet suna iya samun digiri na farko da na biyu da na uku a cikin jami'a.

Sinimar ta ba da shaida sosai a kan kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi na kafa zaman daidai wa daida da kawo alheri da zaman wadata ga jama'ar Tibet da kuma nasararorin da ta samu.(Halima)


1 2