Kwanan baya, ma'aikatar daukar sinima dangane da labarai ta tsakiya ta kasar Sin ta bayar da sinimar tarihi da ke da lakabin " abubuwan da suka faru a da a jihar Tibet". Ta hanyar yin tattaunawa da yin ziyara da wadanda suke da nasaba da abubuwan da masu ba da shaidu da kwararru, an sake maimaita hakikanin halin da ake ciki wajen siyasa da tattalin arziki da zamantakewar al'umma da al'adu da sauransu kafin yin kwaskwarimar dimokuradiya a shekarar 1959 a cikin sinimar wadda ta tayar da martani sosai daga mutanen Tibet.
Tashi Wangdu mai shekaru 73 da haihuwa kuma mai daukar hotuna na kabilar Tbiet ya taba shiga kwaskwarimar dimokuradiya da aka yi. Kafin shekaru 50 da suka wuce, bisa matsayin farko na Tibet wajen daukar hotuna , Mr Tashi Wangdu ya taba daukar hotunan gandun noma mai suna Phalha. Gandun noma mai suna Phalha yana daya daga cikin manyan gandunan noma 12 na masu sukuni na Tibet. Kafin shekaru 50 na karnin da ya wuce, ana iya sifanta gandunan noma na masu sukuni na Tibet da cewar wai "aljanna" da "wuta" . A cikin sinimar da aka dauka, Tashi Wangdu ya bayyana cewa, a shekarar da yake ganin halin da ake ciki na nuna abubuwa masu kyaun gani sosai tare da zalunci da aka yi a cikin wannan gandun noma a karo na farko, ga shi mutum ne da ya fito daga iyali mai fama da talauci sosai ya yi mamaki sosai da sosai. Ya bayyana cewa, lokacin da muka isa gandun noma na Phalha don daukar sinima, mai gandun noma Phalha Wangchug ya riga ya tafi kasar Indiya. Kafin shekaru 50 da suka wuce, mai kula da harkokin wannan gandun noma yana rike da jakuna biyu da ke cike da mabudai, ya bude mana kofofin dakunan gandun noma daya bayan daya domin daukar sinima. Kai, gandun noman nan ba wani abu ba ne sai babban gandun noma kawai, ya cika da wadata sosai. Ga kwalaben giya da abinci iri iri suna cike da dakunan, kuma kwalaben giya na kasashen waje na da yawan gaske tare da alewa da cake da sauransu iri iri da ba a taba gani ba.
1 2
|