Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-18 13:59:53    
Tsagaita bude wuta a lokacin gudanar da gasar wasannin Olympic ta zamanin da

cri
 

Kafin bude gasar wasannin Olympic ta zamanin da, a kan doki kuma tare da rike da wutar da aka kunna a gaban gidan ibada na Olympia a hannunsu, alkalan wasa sun zagaye dukkan daulolin Girka domin ba da umurnin tsagaita bude wuta. A lokacin can, an daina dukkan yake-yake, an bude dukkan hanyoyin da aka toshe a sakamakon yake-yake. Bayan da aka ba da umurnin tsagaita bude wuta, fararen hula na Girka sun fara zuwa Olympia domin shiga gasanni.

A tarihin gasar wasannin Olympic ta zamanin da, an taba saba wa umurnin tsagaita bude wuta, amma an ci tarar wadanda suka saba wa umurnin ko kuma yanke masu hukunci. Umurnin tsagaita bude wuta ya sanya gasar wasannin Olympic ta zama gaggarumin bikin sada zumunci.

Gasar wasannin Olympic ta zamanin da ta bullo ne domin halin da ake ciki a wancan lokaci, wato an shan wahalar yake-yake, an yi gasanni domin nuna wa gumaka girmamawa, amma bullowarta ta nuna cewa, mutane suna matukar fatan samun zaman lafiya. Irin wadannan dalilai ne suka haddasa bullowar gasar wasannin Olympic ta zamanin da da kuma ci gabanta. Yanzu ana shirya gasar wasannin Olympic ta zamanin yau ne domin ci gaba da samun amincewa da juna da zaman lafiya a tsakanin mutane.(Tasallah)


1 2