Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-18 13:59:53    
Tsagaita bude wuta a lokacin gudanar da gasar wasannin Olympic ta zamanin da

cri

In mun yi nazari kan asalin gasar wasannin Olympic ta zamanin da bisa halin da ake ciki a da da kuma a zamanin yanzu, to, muna iya gano cewa, akwai dalilai 3 da suka sa bullowar gasar wasannin Olympic ta zamanin da.

Da farko, an sha ta da yake-yake a tsakanin daulolin Girka ta zamanin da, don neman samun nasara, mutane sun motsa jiki domin horar da jarumai masu karfi, wasannin motsa jiki sun sami bunkasuwa a cikin irin wannan hali, sa'an nan kuma, gasannin da aka shirya sun aza harsashi wajen bullowar gasar wasannin Olympic. Na biyu, an ba da gaskiya ga gumaka da dama tare. A ko wane karon da aka yi bukukuwa domin nuna wa gumaka girmamawa, a kan shirya gangamin addini, inda a kan yi wake-wake da raye-raye da kuma gasanni domin nuna wa gumaka girmamawa. Mutanen Girka suna ganin cewa, Zeus shi ne sarkin gumaka, shi ya sa aka shirya matukar kasaitaccen biki domin nuna masa girmamawa, wannan ya haddasa bullowar gasar wasannin Olympic. Dalili na karshe shi ne saboda akwai dauloli fiye da 200 a Girka a zamanin da, a kan ta da yake-yake a tsakanin wadannan dauloli. Fararen hula na Girka da ke shan wahalar yake-yake suna matukar fatan samun gajeren lokacin da za a tabbatar da zamanin lafiya, shi ya sa mutane suke fatan da sunan gumaka ne za a tsagaita bude wuta a lokacin gudanar da gasar wasannin Olympic, ta haka za a rage yake-yake da kuma fitar da kansu daga wahalhalu.


1 2