Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-17 14:32:58    
Gidan ibada na Dazhaosi da ke arewa da Babbar Ganuwar ta kasar Sin

cri
 

A kan yi wata harkar gargajiya ta addinin Buddha a gidan ibada na Dazhaosi, wato yin rawar Charm, ko kuma yin rawar Ubangiji a bakin fararen hula. Ana shirya wannan harka ne domin kori dodo da murnar samun girbin hatsi da kuma nuna fatan alheri kan samun sa'a da farin ciki a shekara mai zuwa. A watan Mayu da watan Yuni na ko wace shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a kan shirya gaggarumin bikin yin rawar Charm a gidan ibada na Dazhaosi. A lokacin can, mabiyan addinin Buddha su kan sanya tufafi irin na musamman, su kan sa abubuwan rufi fuska domin nuna kama da Ugangiji iri daban daban. A karkashin kide-kiden da aka samar ta hanyar yin amfani da kayayyakin kida irin na musamman na addinin Lama, an fara rawar Charm a tsanake kuma cikin murna. Irin wannan rawa na da ban mamaki da kuma ban sha'awa kwarai.

A lokacin da ake rawar Charm, an fi mai da hankali kan rawar da aka nuna kamar Ubangiji na Baimeishen da na Indiya. Tare da kide-kide masu karfi, wadanda suka sanya abubuwan rufi fuska irin na barewa da shanu sun yi wasa da takobi, sun yi kama da kashe dodo. Jin Cheng, wani babban lama na gidan ibada na Dazhaosi ya yi karin bayani da cewa,

'Saboda an yi kwaskwarima kan gidan ibada na Dazhaosi da kuma kyautata muhallin da take ciki a shekarun baya da suka wuce, dimbin masu yawon shakatawa da kuma masu bin addinin Buddha na gida da na waje sun kawo nan ziyara, sun nuna matukar sha'awa kan rawar Charm da karanta litattafan addinin Buddha da sauran harkokin addinin Buddha.'

A shekarun nan da suka gabata, hukumar jihar Mongolia ta Gida ta zuba kudade da yawa kan yin kwaskwarima kan gidan ibada na Dazhaosi, ta rushe tsoffin gidajen da ke kewayen gidan ibadan, kuma suna cikin hadari da kuma gine-ginen kasuwanci a gefunan hanya, ta haka, gidan ibada na Dazhaosi ya maido da kyan ganinsa na da. Ban da wannan kuma, a yamma da gidan ibada na Dazhaosi, ana adana wani cikakken titi mai tsawon daruruwan shekaru. Wannan titi ya jawo sha'awar darektoci da yawa da su yi fina-finai da kasun wasannin kwaikwayo na talibijin game da labarun da suka faru a zamanin da a wannan titi. Kazalika kuma, kayayyakin da aka yi da hannu, kuma ake sayar da su a titin, kamar kayayyakin gargajiya da zane-zane da abubuwan lu'ulu'u irin na jade da kuma zane-zanen da 'yan kabilar Mongolia suka yi kan fata da kuma kayayyakin tagulla da suka kera, sun shahara sosai.

A shekarun nan da suka zarce, yawan wadanda suka yi bulaguro a gidan ibada na Dazhaosi yana ta karuwa. Game da wannan, Cui Jin, wanda ke yi ziyara a nan, yana ganin cewa, halayen musamman irin na addini shi ne daya da cikin muhimman dalilan da suka sa wannan gida ibada ya jawo dimbin masu yawon shakatawa. Mr. Cui ya ce,

'Baya ga wannan gidan ibada, na zagaya sauran wurare. An wallafi litattafai da yawa, an rarraba su domin ba da gudummowa wajen raya addinin Buddha. Mazauna wurin suna yada al'adunsu, ta haka za a kara fahimta kan al'adunsu da kuma tarihin ko wane gidan ibada a wurin. Dukkansu kayayyakin tarihi na al'adu ne.'


1 2