Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-17 14:32:58    
Gidan ibada na Dazhaosi da ke arewa da Babbar Ganuwar ta kasar Sin

cri

Jihar Mongolia ta Gida mai cin gashin kanta tana bakin iyakar kasar Sin a arewa, inda ake iya ganin kyakkyawan babban filin ciyayi da kuma fahimatar al'adar musamman da 'yan kananan kabilun kasar Sin suka saba bi, sa'an nan kuma, ana bin addinai da dama cikin 'yancin kai a nan. Yau ma za mu kai ziyara ga wani shahararren gidan ibada da ke wannan jiha, wato gidan ibada na Dazhaosi.

Gidan ibada na Dazhaosi yana cikin tsohon bangaren birnin Huhhot, babban birnin jihar Mongolia ta Gida. 'Yan kabilar Mongolia su kan kira shi 'Yikezhao', wato babban gidan ibada. An fara gina shi a zamanin daular Ming ta kasar Sin, wato a shekarar 1580. Shi ne wani gidan ibada na karen kyau. Saboda ana ajiye mutum-mutumin azurfa na Sakyamuni a babban zauren wannan gidan ibada domin nuna girmamawa, shi ya sa a kan kira gidan ibadan 'gidan ibada na Yinfosi', wato gidan ibada da ake ajiye mutum-mutumin azurfa na Buddha a ciki. Sa'an nan kuma, an ajiye dimbin kayayyakin tarihi na al'adu a nan, wadanda suke da matukar daraja wajen nazarin tarihin kabilar Mongolia da kuma al'adunta da addinanta.

Dangane da muhimmin matsayin da gidan ibada na Dazhaosi ke tsayawa a kai a jihar Mongolia ta Gida a harkokin yawon shakatawa, Burenbat, wani shehun malami da ke aiki a cibiyar nazarin ilmin kabilar Mongolia ta jami'ar Mongolia ta Gida, ya yi mana karin bayani da cewa,

'Dubu dubban mazauna birnin sun shiga harkokin addinin Buddha, suna halartar bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin masu ban sha'awa, inda suka yi raye-raye irin na kabilar Mongolia. Na gano cewa, ana wanzar da jituwa a zaman al'ummar kasa a birninmu. Gidan ibada na Dazhaosi ya taka muhimmiyar rawar da ba a iya kyale ta ba a harkokin gadon al'adun addinin Buddha na gargajiya da na kabilar Mongolia, shi ne kuma wani muhimmin bangaren da hukumar jihar Mongolia ta Gida ke dora muhimmanci kan raya shi domin sa kaimi kan bunkasuwar aikin yawon shakatawa.'


1 2