Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-12 18:24:16    
Kai ziyara a lambun al'adu na 'yan kabilar Hui na jihar Ningxia

cri

Wadatuwar kayayyakin tarihi da ake ajiye a lambun al'adu, su ma sun zama kayayyaki masu daraja wajen fahimtar al'adun musulunci. Mr. Xu Wei ya gaya wa wakilinmu cewa, "Yanzu, muna gudanar da hadin gwiwa tare da majalisun musulunci, da kolejojin alkur'ani na musulunci. A 'yan kwanakin da suka wuce kuma, kolejin alkur'ani na musulunci na jihar Ningxia ya nada wannan gidan ajiye kayayyakin gargajiya na al'adu da ya zama sansanin ba da ilmin kaunar da kasar mahaifa ga musulmi, kullum kolejin ya shirya kwas-kwasan limamai da su kawo ziyara a nan bisa lokacin da aka tsaida, don fahimtar ilmin al'adu na kabilar Hui."

Masu aiki a wannan lambun al'adu sun gaya wa wakilinmu cewa, akwai kayayyaki biyu da ke da darajar ambatarsu musamman daga wadannan kayayyakin da ake ajiye da su a nan. Daya daga cikinsu shi ne: wani littafin Alkur'ani da aka haifar da shi a daular Ming ta kasar Sin, wato daga shekarar 1368 zuwa shekarar 1683, har zuwa yanzu, wannan ne wani cikakken littafin Alkur'ani da ya fi da dogon tarihi da aka samu a jihar Ningxia. Wani kaya daban shi ne, samfurorin jiragen ruwa masu kwaikwayon jiragen ruwa na tsohon zamanin Larabawa, da kayayyakin ado da tuffafi na musulmi maza da mata, wadanda Mr. Abdullah Matouk, ministan shari'a na kasar Kuwait, kuma ministan kula da asusun addinai da harkokin musulmi na kasar ya bayar ga lambun al'adu a watan Yuni na shekarar 2007. Wadannan abubuwan kyauta sun shaida yin cudanya da mu'ammala a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa.

Abubuwa da yawa dake gidan ajiye kayayyakin gargajya na tarihi, sun jawo hankulan abokanmu da yawa daga kasashen ketare. Wani jami'I na wannan lambun al'adu Mr. Lei Runze ya gabatar da cewa, "Bayan da aka bude gidan ajiye kayayyaki na tarihi, jakadu da masana daga kasashe masu bin addinin musulunci, ciki har da Kuweit, da Yemen, da Iran, da Pakistan, da Masar, da dai sauransu, sun kawo ziyara a nan daya bayan daya, lallai sun yi farin ciki sosai, har ma suna ganin cewa, wannan abin mamaki ne da aka kafa manyan gine-gine na musulmi kamar haka a babban yankin kasar Sin."

Mr. Lei ya cigaba da cewa, bi da bi ne jami'ai da abokai daga kasashe masu bin addinin musulunci suka bayyana cewa, za su hada kai tare da gidan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi, kuma za su bayar da abubuwan da ke bayyana musulunci, don kara wadatuwar kayayyakin al'adu da ke wurin. Daga baya kuma, Mr. Lei ya bayyana cewa, zai yi kokari tare da masu aiki a nan, don kafa lambun al'adu na 'yan kabilar Hui kamar wata cibiyar taru, da yin tattaunawa, da cudanya a tsakanin musulmi daga gida da waje.

"Dalilin da ya sa muka kafa wannan lambun al'adu shi ne, taimaka wa matafiya daga gida da waje, don su fahimci tarihi da al'adu na kabilar Hui. Bayan haka kuma, bisa wannan tushe, za mu cigaba da habaka lambun al'adu, a nan gaba ba kawai lambun al'adu zai zama wani sansanin sana'o'in yawon shakatawa, da al'adu ba, har ma zai zama wata cibiyar yin taru, da tattaunawa, da cudanya a tsakanin musulmai daga gida da waje. Yanzu, muna cike da shirin kafa cibiyar yin cudanya ta al'adun musulunci, da makarantar koyar da Larabci, da dai sauransu, ta yadda za mu gabatar da wata dama mai kyau wajen yin cudanyar sada zumunci a tsakaninmu da kasashe masu bin addinin musulunci na duniya. A ganina, wannan zai ba da amfani sosai kan aikin bude kofa ga kasashen waje da jihar Ningxia ke yi."


1 2