Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-12 18:24:16    
Kai ziyara a lambun al'adu na 'yan kabilar Hui na jihar Ningxia

cri

Jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui da ke arewa maso yammacin kasar Sin, ita ce jihar da 'yan kabilar Hui ke zaune daya kawai a nan kasar Sin, al'adun musamman da jihar ke da shi, ya sanya jihar Ningxia ta zama wani kyakkyawan wurin da aka fi kallon yanayin rayuwa da kuma al'adun musulmi.

An kafa wannan lambun al'adu a watan Satumba na shekarar 2005, ya zuwa yanzu kuma, shi ne wuri daya kawai da ke iya nuna al'adun kabilar Hui a kasar Sin. Mr. Lei Runze, wani jami'i na wannan lambun al'adu ya gaya mana cewa, "Jihar Ningxia wata jiha ce mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui, wato wani wurin da 'yan kabilar Hui na kasar Sin ke zama tare. Akwai 'yan kabilar Hui da yawansu ya kai kusan miliyan 10 a nan kasar Sin, ciki kuwa sama da miliyan 2.1 daga cikinsu suna zama ne a jihar Ningxia. Amma, a cikin dogon lokaci babu wani wurin da ke iya nuna tarihi, da al'adu na kabilar Hui. Domin cika gibin da ke kasancewa a fannonin yawon shakatawa, da al'adu, gwamnatin jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui ta gina wannan lambun al'adu na 'yan kabilar Hui, da wani gidan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi."

Saboda daidai rawar musamman da lambun al'adu na 'yan kabilar Hui ke taka a fannin al'adu, tun daga aka soma gina sa, sai ya jawo hankali sosai daga gwamnatin wurin. Mr. Lei Runze ya gabatar da cewa, "Kasarmu jamhuriyar jama'ar kasar Sin, wata kasa cewa da ke kunshe da kabilu da dama, kabilar Hui ita ce kuma daya daga cikin wadanda suka fi samun cigaba a fannonin tattalin arziki da al'adu, a waje daya kuma, al'adun kabilar Hui wani iri sabon al'adun kabila ne da aka harfar da shi a sanadiyar hadin kan al'adun musulunci da al'adun gargajiya na daular Han da daular Tang. Gaskiya ne, kafuwar wannan lambun al'adu ba kawai tana biyan bukatu na zamani ba, har ma tana biyan bukatun dan Adam wajen fahimtar al'adun kabilar Hui."

A karkashin jagorancin wannan jami'i, wakilinmu ya shiga lambun al'adu. Kafin babbar kofa, ana iya ganin wani fili da ke iya kunshe da mutane dubu 10. A lokacin bukukuwa, za a yi wake-wake da raye-raye a nan. Mr. Xu Wei, 'dan kabilar Hui da ke aiki a lambun al'adu, ya gaya wa wakilinmu cewa, "Fadin muraba'in lambun ya kai ekoki 20, ciki har da gidan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihn kabilar Hui, da babban dakin al'ada, da kauyen gargajiya na kabilar Hui, da dakin cin abinci na kabilar Hui, da kuma wata cibiyar nune-nunen fasahohi na kabilar Hui, lallai sun kunshe da al'adu, da tarihi, da wake-wake da raye-raye, da kuma ilmin hikimomin al'aumma na kabilar Hui, haka kuma ana iya cewa, wannan lambu shi ne wuri daya kawai da ke iya nune-nunen al'adun kabilar Hui a dukkan fannoni a nan kasar Sin."

Bayan da aka shiga babbar kofa, sai a ga dukkan lambun al'adu a gaba. Da farko, ana iya ganin wani babban gini mai siffar rubutun "Hui" cikin Sinnanci, shi ne gidan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihin kabilar Hui. Bayan da aka shiga wannan gidan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi kuma, sai a yi tamkar yin yawo a doguwar hanya ta tarihi, da fahimtar yunkurin bunkasuwar wayin kai ta kabilar Hui. A nan kuma, ana ajiye kayayyakin bayyanai na abubuwan da, da na littattafai fiye da dubu daya aka samu daga da gida da waje, wadanda ke shafar kabilar Hui, da musulunci, sun nuna muhimman batutuwa biyar, wato asalin tarihi na kafuwar kabilar Hui, da yunkurin wayin kai na musulunci, da al'adun musamman na kabilar Hui ta kasar Sin, da muhimmiyar rawa da kabilar Hui ke taka a tarihin wayin kai na kasar Sin, da kuma kafuwa, da bunkasuwa, da sauye-sauyen kabilar Hui ta jihar Ningxia.

1 2