Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-12 16:46:18    
Ko za a iya tabbatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Somaliya

cri

Na uku, har zuwa yanzu, ba a rasa samun musanyar wuta a tsakanin dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin Somaliya da sojojin gwamnati da na Habasha. A ran 8 ga wata, a kalla dai mutane 15 sun rasa rayukansu a sanadiyyar musanyar wuta da aka yi tsakanin dakarun da ba sa ga maciji da gwamnati da sojojin gwamnatin da na Habasha, a yayin da wasu sama da 50 suka ji raunuka. Har ma a lokacin da ake shawarwari a kasar Djibouti, ba a sami kwanciyar hankali a Somaliya ba.

Tun bayan da yakin basasa ya barke a Somaliya a karshen shekarar 1990, an riga an gudanar da shawarwarin shimfida zaman lafiya sama da 10 a Somaliya tare kuma da cimma yarjejeniyoyi daban daban, amma dukan yarjejeniyoyin sun lalace a karshe ko kuma ko kadan ba a aiwatar da su ba.

Yarjejeniyar da aka cimma a ranar 9 ga watan nan da muke ciki ta nuna cewa, bisa kokarin da aka yi, an sami ci gaba wajen neman daidaita sabani ta hanyar siyasa. Amma duk da haka, ko za a iya tabbatar da sabuwar yarjejeniyar, sai Allah ya ba mu amsa a nan gaba.(Lubabatu)


1 2