Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanku da war haka, barkanmu kuma da saduwa da ku a filinmu na "Afirka a yau", kuma ni ce Lubabatu a yau Alhamis ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.
Masu sauraro, a ran 9 ga watan nan da muke ciki a kasar Djibouti, gwamnatin wucin gadi ta kasar Somaliya ta daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da kungiyar sake 'yantar da Somaliya, wadda ke kin jininta. Jama'ar Somaliya da ke fama da fadace-fadace suna sa rai ga wannan ci gaban da aka samu. Amma duk da haka, idan an yi la'akari da tarihi ko kuma hakikanin halin da ake ciki, to, za a gane cewa, ana fuskantar kalubale mai tsanani a wajen aiwatar da yarjejeniyar. Ko yarjejeniyar za ta iya kawo wa kasar zaman lafiya, ya ci gaba da kasancewa wata babbar tambaya.
Da farko dai, an sami sabanin ra'ayi sosai a tsakanin kungiyar sake 'yantar da Somaliya, dangane da ko za a yi shawarwari tare da gwamnatin wucin gadi.
A watan Satumba na shekarar da ta shige, a birnin Asmara, babban birnin kasar Eritrea, wasu shugabannin kungiyar kotunan Islama wadanda gwamnatin wucin gadin Somalia da sojojin Habasha suka fafatake su, sun kira taron samun sulhu tsakanin al'ummar kasar, inda suka hada kan kungiyoyin daban daban da ke kyamar gwamnatin wucin gadin Somaliya da sojojin Habasha, har ma sun kafa kungiyar sake 'yantar da Somaliya. Tun farkon shekarar da muke ciki, masu sassaucin ra'ayi da ke cikin kungiyar, sun kaura zuwa Djibouti daga Asmara, kuma sun fara shawarwari tare da gwamnatin wucin gadi, a yayin da masu tsattsauran ra'ayi suke ci gaba da kasancewa a Asmara suna kin jinin shawarwarin.
Bayan haka, bayan da masu sassaucin ra'ayi da ke cikin kungiyar sake 'yantar da Somaliya suka bayyana burinsu na yin shawarwari da gwamnatin wucin gadi don daidaita matsalar Somaliya cikin lumana, kungiyar Islama ta matasa, wadda da ma aka bayyana ta a matsayin kungiyar da ke karkashin jagorancin kungiyar kotunan Islama, nan da nan ta sanar da nisanta kanta daga kungiyar, kuma ba ta shiga shawarwarin da aka yi a Djibouti ba.
Na biyu kuwa, yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta nemi MDD da ta girke sojojin kiyaye zaman lafiya a Somaliya cikin kwanaki 120 bayan da yarjejeniyar ta fara aiki, a sa'i daya kuma, Habasha ta janye sojojinta daga Somaliya. Amma bisa halin da ake ciki yanzu, da wuya a cika shi, kuma ana shakkar ko za a iya tabbatar da tsagaita bude wuta, muddin aka gagara wajen biyan wannan bukata.
1 2
|