Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-11 19:12:29    
Ba a sami sakamako a gun taron koli na kungiyar EU da Amurka ba

cri

A kan batun sauyawar yanayi da kungiyar EU da Amurka suke ta gamuwa da sabani mai tsanani, a gun taron manema labaru da aka yi bayan taron, Janez Jansa, firayim ministan Slovenia da ke shugabantar kungiyar EU a wannan zagaye ya bayyana cewa, kungiyar EU da Amurka sun gamu da rikici kan rage fitar da iska mai dumama yanayi da sauran batutuwa. Amma shugabannin bangarorin 2 sun nanata daidaita batun sauyawar yanayi da sauran muhimman kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta tare. Sa'an nan kuma, Mr. Barroso, shugaban kwamitin kungiyar EU ya ce, a matsayin yankuna mafiya ci gaba a duniya, ya kamata Amurka da kungiyar EU su kara yin hadin gwiwa kan rage fitar da iska mai dumama yanayi. Mr. Bush kuwa ya yi alkawarin cewa, watakila Amurka za ta cimma daidaito kan batun sauyawar yanayin duniya tare da bangarorin da abin ya shafa kafin ya cika wa'adin aikinsa.

Ban da wannan kuma, Mr. Bush ya yi amfani da halartar taron kolin ya fara ziyararsa ta yin ban kwana a Turai. Yadda za a sassauta rikicin da kungiyar EU da Amurka suke ta fuskanta da kuma daidaita karuwar rarar kudin da kungiyar EU ta samu daga wajen yin ciniki da Amurka a shekarun baya za su ci gaba da dame Mr. Bush a kan hanyar ziyararsa.(Tasallah)


1 2