Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-11 19:12:29    
Ba a sami sakamako a gun taron koli na kungiyar EU da Amurka ba

cri

Ran 10 ga wata, a birnin Brdo na kasar Slovenia, an rufe taron koli na kungiyar tarayyar Turai wato EU da kasar Amurka, wanda aka yi kwana guda ana yinsa. A gun taron, bangarorin 2 sun tattauna yin hadin gwiwar tattalin arziki da yaki da ta'addanci da batun nukiliya na kasar Iran da kuma samar da isasshen makamashi da sauyawar yanayi da farashin abinci. Manazarta suna ganin cewa, kamar yadda suka yi a da, bangarorin 2 ba su sami hakikanan sakamako a gun wannan taron koli ba, sun fi nuna burinsu a maimakon yin alkawari.

Tun da har zuwa yanzu, kungiyar EU da Amurka kawayen juna ne a harkokin siyasa, haka kuma suna kasancewa abokai mafi girma da suke yi ciniki a tsakaninsu da kuma wanda ya fi zuba wa juna jari. Bayan da aka tabbatar da tsarin yin tattaunawa a kan lokaci kamar yadda aka tsara a shekarar 1990, taron koli na kungiyar EU da Amurka ya zama muhimmin tsarin yin mu'amala a tsakanin manyan jami'an Turai da Amurka. A gun taron da aka yi a shekarar bara, bangarorin 2 sun daddale yarjejeniyoyi da dama, sun kuma yi shirin kafa kwamitin kula da tattalin arziki a ketaren tekun Atlantic domin sa ido da ba da jagoranci da kuma inganta huldarsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki. Taron koli da aka yi wannan karo ya zama na karshe da Mr. Bush ya halarta a matsayin shugaban Amurka. Makasudinsa shi ne shawo kan kawayen Amurka a Turai da su dauki matakan musamman kan Iran, ya kuma nemi kungiyar EU da ta mara masa baya kan kafa tsarin tsaron kasa daga harin makamai masu linzami a gabashin Turai.

Amma duk da haka, kungiyar EU ba ta nuna sha'awa sosai kan wannan shugaban Amurka da zai cika wa'adin aikinsa ba da dadewa ba. Alal misali, Amurka tana fatan kasashen Turai za su taka muhimmiyar rawa kan batun Iran da ke shafar moriyar Turai da Amurka duka bayan da sabon shugaban Amurka ya kaddamar da aikinsa a watan Janairu na shekara mai zuwa. Amma a cikin sanarwar hadin gwiwa da suka bayar bayan taron, kamar yadda suka yi a da, bangarorin 2 sun yi kira ga Iran da ta sauke nauyin da kasashen duniya suka danka mata a kan batun nukiliya, ciki, har da yin hadin gwiwa da Hukumar makamashin nukiliya ta duniya daga dukkan fannoni da kuma daina gudanar da shirin tace sinadarin uranium kawai. Batun nukiliya na Iran mai sarkakkiya ya sanya kungiyar EU da Amurka ba su iya warware shi a gun taron koli sau daya kawai ba.

Sa'an nan kuma, sanarwar hadin gwiwa da aka bayar bayan taron ba ta shafi batun kafa tsarin tsaron kasa daga harin makamai masu linzami da Amurka ta yi ta yayata a kasashen gabashin Turai ba. Manazarta sun nuna cewa, ko da yake Turai da Amurka kawaye ne tun can da, amma suna fuskantar sabani a moriyarsu ko kuma rikici a wasu fannoni. Balle ma har kullum kasashen yammacin Turai ba su maraba da Mr. Bush, wanda ya ta da yakin Iraq. Shi ya sa a lokacin da ya rage sauran watanni 7 da Mr. Bush ya cika wa'adin aikinsa, shugabannin kungiyar EU sun fara mai da hankulansu da kuma nuna fatan alheri kan wanda zai maye gurbinsa.

1 2