Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-10 16:33:28    
Jihar Mongolia ta gida tana dukufa kan shawo kan kwararowar hamada don tabbatar da samun iska mai inganci a birnin Beijing

cri

Kuma Mr. Li ya ce, ban da karfafa aikin shawo kan kwararowar hamada a duk fadin jihar, jihar ta daidaita hamadar HunShanDaKe, masomin samar da rairayi da ke mafi kusa da birnin Beijing. Kuma bisa kokarin da aka yi, yanzu muhallin halittu na wannan hamada ya samu kyautatuwa a bayyane. Kuma ya kara da cewa, "A 'yan shekarun nan da suka gabata, an samu sakamako mai kyau a bayyane wajen daidaita hamadar HunShanDaKe. A bakin kudancin hamadar, an riga an samu wani yankin bishiyoyi da tsawonsa ya kai kusan kilomita 400, kuma fadinsa ya kai daga kilomita 1 zuwa kilomita 10."

Ban da wannan kuma Mr. Li Shuping ya bayyana cewa, ba kawai aikin shawo kan kwararowar hamada da jihar Mongolia ta gida ke yi ya ba da tabbaci ga samar da kyawawan sharuda ga ingancin iskar birnin Beijing a lokacin yin gasar wasannin Olympics ba, har ma ya kawo wa manoma da makiyaya na wurin alherin a zo a gani, kuma ya samu amincewa sosai daga wajensu. Chaogebator, wani makiyayi na birnin Xilingol na jihar yana daya daga cikinsu. Kuma ya gaya mana cewa, "Kaura daga filin ciyayi ya iya sassauta matsin lamba da aka kai wa filin ciyayi, kuma ciyayi za su samu damar yin girma. A wadannan shekaru biyu da suka gabata, ana iya gano wannan sakamako mai kyau a bayyane, ko da aka gamu da matsalar fari, amma dabbobi suna da isasshen abinci, haka kuma filin ciyayi cike yake da launin kore."


1 2