Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-10 16:33:28    
Jihar Mongolia ta gida tana dukufa kan shawo kan kwararowar hamada don tabbatar da samun iska mai inganci a birnin Beijing

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan cewa, jihar Mongolia ta gida ta kasar Sin tana dukufa kan shawo kan kwararowar hamada domin tabbatar da samun iska mai inganci a birnin Beijing a lokacin yin gasar wasannin Olympics. To yanzu ga cikakken bayani.

Jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai ta kasar Sin tana daya daga cikin jihohin da aka fi samun yawan hamada a kasar. Wannan hamada ta zama muhimmin masomi ne na samar da kura a yankunan da ke arewacin kasar Sin, wanda yake yin illa sosai ga ingancin iskar jihar da kuma birnin Beijing da ke kusa da ita. Domin fama da kura da kuma tabbatar da samun iska mai inganci a birnin Beijing a lokacin yin gasar wasannin Olympics a ciki, a 'yan shekarun nan da suka gabata, har kullum jihar Mongolia ta gida tana mayar da aikin shawo kan kwararowar hamada da kuma kara dasa bishiyoyi a matsayin wani mihimmin aiki.

Li Shuping, mataimakin shugaban hukumar kula da bishiyoyi ta jihar ya bayyana cewa, "A 'yan shekarun nan da suka gabata, jihar Mongolia ta gida ta samu sakamako mai kyau a bayyane a cikin ayyukan shawo kan kwararowar hamada. Da farko, an samu babban ci gaba wajen hana kwararowar hamada. Bisa sakamakon bincike da aka yi, an ce, yanzu fadin hamada na jihar ya ragu da kadada miliyan 1.6 bisa na shekara ta 1999, kuma fadin kasa mai rairayi ya ragu da kadada dubu 480. Ban da wannan kuma, an sa kaimi sosai kan sauyin hanyar zaman rayuwa na manoma da makiyaya da ke yankunan hamada, ta hanyoyin mayar da gonaki don su zama gandun daji, da mayar da makiyaya don su zama ciyayi da dai sauransu, an fara kiwon dabbobi a gida a maimakon a waje, ta yadda aka kara moriyar da ake samu a wannan fanni."

1 2