Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-06 16:39:30    
Sin ta soma tsara shirin sake gina yankunan da bala'in girgizar kasa ta shafa

cri

Aminai 'yan Afrika, wani jami'in ma'aikatar kula da harkokin gida gidaje da raya birane da kauyuka ta kasar Sin ya fayyace jiya Alhamis a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin ta rigaya ta soma tsara shirin sake gina yankunan da bala'in girgizar kasar ya shafa, wato ke nan tana cikin shirin daukar shekaru uku don farfado da manyan ayyukan tushe da kuma gidajen kwana na wuraren da bala'in girgizar kasa ta shafa daidai kamar yadda suka kasance kafin aukuwar bala'in. Daga kuma za ta dauki tsawon shekaru biyar wajen kyautata zamantakewar al'umma da kuma bunkasa tattalin arziki na wuraren da bala'in ya shafa daga dukkan fannoni.

An labarta cewa, jiya dai ofishin yada labarai na majaliar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya wani taron manema labararu, inda mataimakin ministan kula da harkokin gina gidaje da raya birane da kauyuka na kasar Sin Mr. Qi Ji ya bayyana cewa, aikin wallafa shirin sake gina yankunan da ke fama da bala'in yana shafar fannoni uku wato na tsarin sake gina birane da garuruwa, da raya kauyuka da kuma na gina gidajen kwana.


1 2 3