Da yake birane da garuruwa sun samu babbar hasara a cikin girgizar kasar, shi ya sa tsarin gina birane da garuruwa ya fi janyo hankulan mutane. Game da wannan dai, Mr. Qi Ji ya furta cewa: " Babbar manufar tsarin sake gina birane da garuruwa bayan bala'in, ita ce: kaddamar da tsarin shimfida birane da gudunmomi da kuma garuruwa na wuraren da bala'in girgizar kasar ya shafa da kuma shirin girman sikelin sake gina su; da zabar sabbin wuraren gina gundumomi da garuruwa, wadanda ake bukatar kaurar da su saboda sun fi fama da bala'in da kuma shirin girman sikelin gina su; da kaddamar da shirin shimfida hanyoyin zirga-zirga da muhimman ayyukan tushe da kuma kimanta barnar da bala'in ya yi wa shahararrun wuraren tarihi a matakin gwamnatin kasa da dai sauransu.
Ban da wannan kuma, Mr. Qi Ji ya ce, za a dora muhimmanci kan sake gina gidajen kwana na birane da garuruwa da ke wuraren da bala'in girgizar kasa ya shafa. Mr. Qi Ji yana mai cewa: ' Ayyuka uku ne za a yi, wato na farko :a shirya birane da gundumomin da bala'in ya rutsa da su don su yi bincike daga dukkan fannoni kan yanayin gidajen kwana da suka lalace sakamakon bala'in ; Na biyu : a fito da ma'aunin sake gina gidajen kwana da kuma na girman sikelin inganta su ; Aiki na uku shi ne : ba da ra'ayoyi ga hukumomin da abin ya shafa yayin da suke yanke shawarar sake gina gidajen kwana na birane da garuruwa bayan bala'in'.
1 2 3
|