Babbar girgizar kasa da aka samu a lardin Sichuan na kasar Sin ta yi sanadiyyar jikata mutane fiye da dubu 300, wadanda suka kawo matsi mai nauyi ga asibitoci na lardin Sichuan. Domin warkar da mutanen da suka ji rauni yadda ya kamata, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar kai wa mutanen da suka ji rauni zuwa sauran wurare domin warkar da su. Ya zuwa yanzu, an riga an kai mutanen da suka ji rauni fiye da dubu 10 zuwa larduna, da jihohi da ke da ikon tafiyar da harkokinsu da kansu, da biranen da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin take shugabanta kai tsaye da yawansu ya kai 20, inda aka tsugunar da su da kuma warkar da su yadda ya kamata.
Gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan aikin warkar da mutanen da suka ji rauni sakamakon girgizar kasa, kasar Sin ta soke kudin likitanci da suke biya, domin tabbatar da warkar da su cikin lokaci.
A birnin Shijiazhuang da ke arewacin kasar Sin, darektan hukumar kiwon lafiya da ke kula da harkokin tsugunar da mutanen da suka ji rauni, wato Mr. Yang Xinjian ya bayyana cewa, lardin Hebei ya riga ya shirya asibitoci 6 domin karbar mutanen da suka ji rauni sakamakon girgizar kasa. Ya ce,
'Wadannan asibitoci 6 sun fi kyau a duk lardin Hebei. Za a kai masu jin rauni zuwa asibitoci daban daban bisa ga halin da suke ciki, mun riga mun shirya likitoci da sauran ma'aikata da suka fi kwarewa gare su, za mu warkar da su yadda ya kamata. Masu jin rauni sun iso lardin Hebei ne kamar sun dawo gidajensu, muna kula da su kamar iyalanmu.'
1 2
|