Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-04 15:13:39    
Mai kare fadar "The Potala" ta birnin Lhasa mai suna Jampa Kelsang

cri

Wajen kiyaye tsafin da ake kira "Tangka" da nafsin "Pattra Sutra", kwararrun kiyaye kayayyakin tarihi na gida da na waje sun kuma amince da aikin kiyaye kayayyakin tarihi da aka yi . Alal misali, a duk duniya, nafsin "Pattra Sutra" kadan ne da aka tanada yanzu, irin wannan nafsin da aka rubuta a kan ganyayen bishiyoyi an shigo da su a Tibet ne daga kasar Indiya da kasar Nepal, bisa sakamakon kiyaye su cikin wuya sosai, a kasar Indiya, an kuma rasa su duka duka, amma a fadar The Potala, ana jerin gaba a duniya wajen kiyaye su da yin nazari da su. Mr Jampa Kelsang ya bayyana cewa, musamman ne kasar Sin ta kafa cibiyar yin bincike a kai, yanzu, hukumomin kasar Indiya da Japan da sauran hukumomin da abin ya shafa suna son yin hadin guiwa da fadar, ya bayyana cewa, a jihar Tibet, ana mai da hankali sosai ga yin rajistar nafsin "Pattra Sutra" da kiyaye shi, kuma musamman ne aka kafa ofishin kula da harkokin, mun sami nafsin "Pattra Sutra" daga kasar Indiya, dole ne mu kiyaye shi sosai da sosai.

Bisa albarkacin gyare-gyaren da aka yi a kan fadar, masu yawon shakatawa sai kara yawa suke yi, wannan ya kawo cikas ga kiyaye fadar, shi ya sa Mr Jampa Kelsang ya sami hanyar kiyaye shi, wato ya kayyade yawan masu yawan shakatawa, ya ce, ba daga 'yan shekarun nan da suka wuce da muka gabatar da shawarar ba, a gaskiya dai daga ranar 1 ga watan Mayu na shekarar 2003, mun soma kayyade yawan mutanen da za su kai ziyara a fadar.

Amma wasu mutane na kasashen duniya sun rubuta wasiku ga kungiyar Unesco ta Majalisar Dinkin Duniya, inda suka bayyana cewa, kasar Sin ba ta yin kokarin kiyaye fadar ba. A shekarar 2003, Mr Jampa Kelsang ya gayyaci jami'an kungiyar da su yi bincike a fadar, sakamakon da suka samu ya shaida cewa, zargin da aka yi ba daidai ba ne.(Halima)


1 2