Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-04 15:13:39    
Mai kare fadar "The Potala" ta birnin Lhasa mai suna Jampa Kelsang

cri

Wani tsoho mai shekaru 65 da haihuwa na kabilar Tibet mai suna Jampa Kelsang shi ne shahararren kwararren kare al'adun Tibet na kasar Sin, ya dau nauyin shugaban ofishin kula da harkokin fadar "The Potala" bisa wuyansa har cikin shekaru 19, ya ba da gudumuwa sosai ga kiyaye wannan siton tanada kayayyakin al'adu masu daraja sosai.

Da aka haifi Mr Jampa Kelsang ba da dadewa ba, sai mahaifiyarsa ta rasu, bayan wasu shekaru, mahaifinsa shi ma ya rasu. Kawunsa ya ciyar da shi. Mr Jampa Kelsang bai sami damar yin karatu ba bisa dalilai da yawa, wannan abin bakin ciki ne gare shi a cikin duk rayuwarsa. Amma ya yi kokari sosai, tun daga lokacin da ya cika shekaru 16 da haihuwa, ya sami damar nuna sinima ga makiyaya da manoma a wurare daban daban cikin shekaru 30 da suka wuce, wannan ya sa makiyaya suka bude idannunsu, kuma ya sa Mr Jampa Kelsang ya kware sosai wajen yin magana da harshen Sinanci.

A shekarar 1988, Mr Jampa Kelsang ya bar aikinsa na nuna sinima. A shekarar 1989, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta ware kudaden da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 55 don yi wa fadar "The Potala" kwaskwarima. Mr Jampa Kelsang ya shiga aikin kwaskwarima, ya yi aiki wurjanjan, shi ya sa aka yi masa yabo sosai da sosai. A wancan lokaci, an yi bukatar samun wani shugaban kula da harkokin fadar "The Potala", sai aka gabatar da shi don ya dauki nauyin nan, amma , a lokacin farko, bai yarda ba, ya bayyana cewa, da farko, na ki daukar nauyin nan ba tare da sassauci ba, ina dalilin da ya sa haka? Duk saboda a wancan lokaci, ba a yi rajistar kayayyakin da aka tanada a fadar ba, shi ya sa na ji tsoron daukar aikin nan. Matata da dana dukansu sun ce, "kada ka shiga aikin", sun kuma yi mini cewa, a nan gaba, idan mun sami wadata, watakila sauran mutane za su yi magana cewa, mun sami wadata ne saboda kayayyakin da muka sata a fadar The Potala.

Amma a karshe dai, bisa shawo kan da shugabanninsa da sauran abokansa suka yi masa, Mr Jampa Kelsang ya shiga aikin, wato ya dau nauyin zama shugaban kula da harkokin fadar "The Potala", daga nan sai ya shiga aikin sanya masa alfahari tare da damuwa. Game da alfaharin da ya yi, duk saboda fadar The Potala tana bisa tsarkakken matsayi a cikin jama'ar Tibet, kowane kayan da aka tanada a fadar na da daraja sosai da sosai, ya dau nauyin aikin a wurin, wannan abin alfahari ne sosai da sosai. Amma yana damuwa sosai duk saboda wurin na da muhimmanci sosai, ba zai yi kasala ko kadan ba wajen aiki. A cikin shekaru fiye da goma, ya yi kokari sosai, bayan da ya dau nauyin aiki, sai nan da nan ya yi rajistar kayayyakin da aka tanada a fadar, sa'anan aka sami adadinsu , ya kuma kiyaye zane-zanen da aka yi a jikin bangunan fadar da nafsin "Pattra Sutra" da bangunan fadar, don kada masu kai ziyara su lalace su.


1 2