Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-04 12:59:01    
Gasar wasannin Olympic ta zamanin da da kuma mata

cri

Hukuncin da mahukuntan Girka ta zamanin da ya yanke wa matan da suka saba wa ka'idoji suka kalli gasar wasannin Olympic ta zamanin da ya fi sauran hukuncin da aka yanke wa masu laiffufuka muni, haka kuma yana da nasaba da addini. Amma babban dalilin da ya sa aka kebe mata daga gasar wasannin Olympic ta zamanin da shi ne domin nuna bambanci ga mata. Matsayin da mata ke tsayawa a kai ya yi kasa kwarai a Girka ta zamanin da a karni na 11 kafin haihuwa Annabi Isa A.S. zuwa karni na 9 kafin haihuwar Annabi Isa A.S.. Mata na kasancewa tamkar dukiya ce da maza ke mallaka kawai. An gwada darajarsu da yawan dabbobib gida.

A sakamakon bunkasuwar tsarin bauta da kuma tabbatar da tsarin mallakar abubuwa, ko da yake tilas ne wani namiji ya auri wata mace kawai bisa tsarin da aka aiwatar a Girka ta zamanin da, amma mata ba su da iko ko kadan, ba su da ikon gadon dukiyoyi, ba su iya shiga harkokin zaman al'ummar kasa ba. Mata dattijai su ne uwar yara da uwar gida mai kula da harkokin gida da kuma bayi kawai a idon maza a Girka ta zamanin da. Shi ya sa a daulolin Girka ta zamanin da da aka aiwatar da tsarin bauta, mata ba su da ikon zabe bisa dokoki. A Athens, a lokacin da aka haifi wani jariri, za a rataya wani zoben da aka saka da rassan icen zaitun a kofar gida, wannan ya yi hasashen cewa, farin ciki ya sauka a wannan gida. Inda wani ya ga dan kwali da aka saka da ulu a kofar wani gida, to, wannan mutum ya gudu, saboda wannan ya yi hasashen cewa, Ubangiji bai kiyaye wannan gida ba, an haifi wata jaririya banza dazun nan. Kazalika kuma, a daulolin Girka ta zamanin da da aka aiwatar da tsarin bauta, mata ba su da ikon samun ilmi da kuma shiga wasannin motsa jiki ba.(Tasallah)


1 2