Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-04 12:59:01    
Gasar wasannin Olympic ta zamanin da da kuma mata

cri

A gun gasannin wasannin Olympic na zamanin da, an tsara tsauraran kayyadewa da yawa, ciki, akwai wani batu na cewa, an hana mata su shiga gasar wasannin Olympic. An hana dukkan mata su shiga gasanni, ko kuma kallon gasanni, sa'an nan kuma, an tsara wata ka'idar cewa, za a kashe matan da suka kalli gasar wasannin Olympic. Amma don me a? kebe mata daga gasar wasannin Olympic ta zamanin da? Yanzu bari mu kara saninmu kan wannan fanni tare.

Wasu suna ganin cewa, dalilin da ya sa aka hana mata su shiga ko kuma kalli gasar wasannin Olympic ta zamanin da shi ne domin yana da nasaba da addini. Ana ganin cewa, idan aka baiwa mata damar taka rawa a gun wadannan kasaitattun gasanni, to, za su raunana karfin jarumai maza, haka kuma, wannan zai kasance sabo. Shi ya sa hana mata su shiga gasar wasannin Olympic ta zamanin da ya zama wata al'adar da aka saba bi. An fara binta tun daga farko.

Wasu suna ganin cewa, matsayin da mata suke tsayawa a kai a harkokin zaman al'ummar kasa a kasar Girka ta zamanin da, shi ne dalili mafi muhimmanci da ya haddasa hana mata shiga ko kuma kallon gasar wasannin Olympic ta zamanin da.


1 2