Don jama'ar da ke fama da bala'in su iya kaura zuwa kyawawan gidajen wucin gadi tun da wuri, larduna da biranen da ke daukar nauyin ba su taimako suna ta gaggauta kera kayayyakin gidajen wucin gadi da jigilarsu da kuma harhada su. A wani kamfanin da ke daukar nauyin kera kayayyakin gidajen wucin gadi da ke birnin Yantai na lardin Shandong, ma'aikata suna matukar kokarin aiki. Li Changzhi, shugaban wata ma'aikatar da ke cikin kamfanin, ya ce,"Ma'aikata suna kokarin aiki cikin himma da kwazo, kowanensu na son ba da nasu taimako ga jama'ar da ke fama da bala'in. Kome wahalar da muke sha ba za ta wuce wahalhalun da ke gaban jama'ar da bala'in ya shafa ba, kuma kome gajiyarmu ba za ta fi ta masu aikin agaji ba. Muna hada kanmu sosai, don muna son ba da taimakonmu wajen farfado da gidaje ga jama'ar da bala'in ya shafa."
A ran 2 ga wata, a garin Chenjiaba da ke lardin Sichuan, jama'a sama da 1,000 da girgizar kasa ta shafa sun kaura zuwa gidajen wucin gadi da aka gama harhada su. Wata mazauniyar gidan ta ce,"Wannan ya fi tanti sosai, ba zafi. Yau yawan zafi ya kai kimanin maki 40 a cikin tantuna, amma ga shi a nan, ba zafi. Ko da yake girgizar kasa ta galabaitar da mu, amma bisa goyon bayan da jama'ar duk kasar Sin suke nuna mana, ya kamata mu ci gaba da zaman rayuwarmu da karfin zuci."
Bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, ana ta harhada karin gidajen wucin gadi a yankunan da girgizar kasa ta shafa. Gwamnatin kasar Sin ta kuma bayyana cewa, za ta dinga kyautata gidajen, ta yadda za su iya biyan bukatun jama'a.(Lubabatu) 1 2
|