Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-03 18:59:01    
Sin na iyakacin kokarin samar da gidajen wucin gadi ga jama'ar da girgizar kasa ta galabaitar da su

cri

Babbar girgizar kasa da ta afkawa lardin Sichuan na kasar Sin ba ma kawai ta yi sanadiyyar mutuwar dimbin jama'a tare kuma da jikkata wasu masu yawan gaske ba, har ma ta lalata gidajen jama'a masu yawa. Ko da yake gwamnatin kasar Sin ta samar da tantuna da gidajen wucin gadi ga jama'ar da girgizar kasar ta shafa, amma duk da haka, yanayin zaman rayuwarsu ba shi da kyau sosai. Don daidaita matsalolin da suke fuskanta, kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta dauki alkawarin samar musu da gidajen wucin gadi da yawansu ya kai miliyan 1 da dubu 500 cikin watanni uku. A halin yanzu kuma, ana kokarin gudanar da aikin.

Bisa labarin da muka samu da dumi-duminsa, an ce, ya zuwa yanzu, an riga an kwashe jama'a sama da miliyan 15 da girgizar kasa ta shafa tare kuma da sake tsugunar da su. Don kyautata yanayin zaman rayuwarsu, kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar cewa, yayin da ake samar da dimbin tantuna ga yankunan da girgizar kasa ta shafa, an kuma bukaci larduna da birane 21, ciki har da lardunan Guangdong da Hebei da kuma birnin Beijing, da su ba da taimako ga garuruwan da girgizar kasa ta shafa da ke cikin lardunan Sichuan da Gansu da kuma Shanxi, kuma su samar da gidajen wucin gadi da yawansu ya kai miliyan 1 da dubu 500 a gare su cikin watanni uku.

Kwanan baya, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyarar musamman ga garin Langfang da ke lardin Hebei, don samun fahimtar yadda ake kera kayayyakin gidajen wucin gadi. Wata masana'antar da ke birnin na daukar nauyin kera kayayyaki na gidajen wucin gadi 6000 da kuma harhada su. Shugaba Hu Jintao ya fada wa ma'aikatan masana'antar da cewa,"A halin yanzu, tsugunar da jama'ar da girgizar kasa ta shafa ya zama aiki mafi muhimmanci yayin da ake ba da agaji, kuma babbar matsala a gabanmu ita ce karancin gidajen wucin gadi. Gaggauta kera kayayyakin gidajen wucin gadi muhimmiyar shawara ce da gwamnatin kasar Sin ta yanke wajen daidaita matsalolin da ke gaban jama'a da ke fama da bala'in. Muna fatan bayan kun isa yankunan da girgizar kasa ta shafa, za ku gaggauta ayyukanku, ku sauke nauyin da aka danka muku yadda ya kamata, ta yadda jama'ar da ke fama da bala'in za su iya kaura zuwa sabbin gidajensu tun da wuri."


1 2