Don aiwatar da manyan ayyuka na taimaka wa kasashen Afrika, sanarwar Yokohama ta gabatar da shirin aikin Yokohama, inda ta mayar da gina manyan ayyuka da zuba jari ga cinikayya da yawon shakatawa da raya sha'anin noma da kauyuka da ba da ilmin tushe da aikin likitanci da shimfida zaman lafiya a shiyya shiyya da maganin sauye-sauyen da aka samu wajen sararin samaniya da muhalli bisa manyan ayyuka na ba da taimako.
A bikin rufe taron, firayim ministan kasar Japan Mr Fukuda Yasuo ya kuma sake karfafa a kan sakamakon da aka samu a gun taron, inda ya bayyana cewa, taron ya kara kyautata huldar da ke tsakanin kasar Japan da kasashen Afrika zuwa wani sabon matsayi. A gun taron kuma, shi kansa ya yi alkawari cewa, za a samar wa kasashen Afrika rancen kudi na dogon lokaci tare da samun dan ruwa kawai wanda yawansa zai kai kudin Amurka biliyoyi, kuma kafin shekarar 2012, taimakon da za a samar wa kasashen Afrika zai kara ninki daya.
Amma kafofin watsa labaru na kasar Japan sun bayyana cewa, ko gwamnatin Japan za ta iya cim ma burin sabbin manyan tsare-tsare na samar wa kasashen Afrika taimako? Wannan ne ba a iya kimantawa ba . a hakika dai ne, ayyukan da gwamnatin Japan ta ke yi wajen ba da taimako ga samun bunkasuwar Afrika har wa yau dai ba su sami cikakken goyon baya a cikin kasar ba, sa'anan kuma, gamayar kasa da kasa suna taimakawa kasashen Afrika kuma suna samun bunkasuwa ta hanyoyi daban daban, matsayin taron kasa da kasa kan batun ba da taimako ga raya kasashen Afrika a Tokyo ya riga ya ragu wajen harkokin ba da taimako ga kasashen Afrika.
A lokacin da wani jami'in harkokin waje na kasar Japan ya yi magana kan batun ba da taimako ga kasashen Afrika, ya bayyana cewa, kawar da talauci da mganin sauye-sauyen da aka samu wajen sararin samaniya da rikicin abinci da aka samu yanzu dukkansu batu ne da duniya ke daidaitawa cikin wuya sosai, ko da yake firayim ministan kasar Japan ya tsara manufar hakika ta ba da taimako ga kasashen Afrika, amma in kasar Japan ita kadai za ta yi, to ba za ta cim ma burin ba.(Halima) 1 2
|