Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-02 16:02:45    
An rufe taro a karo na hudu na kasa da kasa kan batun raya kasashen Afrika a birnin Toky

cri

A ranar 30 ga watan jiya, a birnin Yokohama da ke bakin tashar ruwa ta kasar Japan, an yi bikin rufewar taro a karo na hudu na kasa da kasa kan batun raya kasashen Afrika wanda aka yi kwanaki uku ana yinsa. Taron ya zartas da sanarwar Yokohama da shirin aikin Yojkohama da wata takarda daban, wato takardu uku ken nan, inda aka tsai da fasali a bayyane ga gwamnatin kasar Japan a kan batutuwan da suka hada da kafa manyan ayyuka don taimaka wa kasashen Afrika a nan gaba da kawar da talauci da cim ma burin shekaru dubu na Majalisar Dinkin duniya da maganin sauye-sauyen yanayin sararin samaniya.

Gwamnatin Japan da Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomi su ne suka shirya taron kasa da kasa na raya kasashen Afrika a Tokyo cikin hadin guiwa, a shekaru biyar biyar ana kiran taron sau daya. Wakilan da suka zo daga kasashen Afrika fiye da 50 da na hukumomin kasa da kasa 55 da na kungiyoyin kasashen Afrika 16 sun halarci taron, an bayyana cewa, wannan ne taron kasa da kasa mafi girma da gwamnatin Japan ta shirya har zuwa yau.

Sanarwar Yokohama da taron ya zartas da ita ana kiran ta cewar takardar siyasa dangane da tarimakon da gwamnatin Japan za ta yi wa kasashen Afrika a nan gaba. Sanarwar ta nuna yabo mai yakini ga sakamakon da kasashen Afrika suka samu a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce bisa karfinsu na kansu wajen siyasa da tattalin arziki, a sa'I daya kuma, ta mai da hankali sosai ga batutuwan da suka kawo kalubale mai tsanani ga raya tattalin arzikin kasashen Afrika a sakamakon kara karuwar yawan mutanen babbar nahiyar Afrika da kara tsananin rashin aikin yi a kauyuka da birane da samun ciwace-ciwace masu yaduwa cikin tsanani da kara hauhawar farashin hatsi a duk duniya. Sanarwar ta bayyana cewa, gamayyar kasa da kasa kamata ya yi su samar wa kasashen Afrika wajababben agaji ta yadda za su taimaka musu wajen raya tattalin arziki da cim ma burin samun bunkasuwa cikin shekaru dubu don kawar da talauci da maganin sauye-sauyen da aka samu wajen sararin samaniya da sauran kalubalen da suke fuskanta.


1 2