
Bisa bukatun nan ne, gidan CCTV na kasar Sin ya kebe lokacinsa na shirya shirye-shirye domin jama'a, masana da yawa sun ba da lacca kan abubuwa dangane da shahararrun al'adun kasar Sin a cikin shirye-shiryen TV don fadakar da jama'ar farar hula. Wata mai ba da lacca a shirye-shiryen TV mai suna Yu Dan ta bayyana cewa, da yake zamanin da muke ciki ya sauya sosai, shi ya sa mutane suke kara jan zuciya ba bisa hakikanan abubuwa ba tare da rashin fahimta, saboda haka ya kamata mu nemi gaskiya daga abubuwa na da.
Wani shehun malami na jami'ar koyar da ilmin yada labarai ta kasar Sin Mr Yuan Qingfeng ya bayyana cewa, aikin nan aiki ne na sake kimanta darajar shahararrun littattafan tarihi. A gaskiya dai ana soma aikin daga karshen shekaru 70 na karnin da ya shige.
Wannan shehun malami ya bayyana cewa, dukkan mutane na kowane zamani suna iya neman sanin asalinsu daga al'adun gargajiyarsu, kuma a lokacin samun bunkasuwa, za su iya waiwayon abubuwan da aka yi a da, haka kuma ga rayukansu da al'ummarsu da al'adunsu, sa'anan kuma suna kara karfinsu na dosawa gaba daga waiwayon .(Halima) 1 2
|