Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-28 17:21:17    
Al'adun gargajiya sun kara jawo sha'awar mutane a kasar Sin

cri

A kasuwannin sayar da littattafai na kasar Sin, ana kara sayar da shahararrun littattafai na gargajiya da na tarihi, haka kuma ana kara mai da hankali ga abubuwan da aka tanada a cikin shirye-shiryen TV da Internet da sauran kafofin yada labarai . An gaya wa manema labaru cewa, a zamanin da muke ciki, mutanen kasar Sin suna son gidansu a zuciya da kuma samun karfi na dosawa gaba daga al'adun gargajiya na zamani tun shekaru aru aru.

A gun taron yin kwangilar sayen littattafai na Beijing da aka shirya ba da dadewa ba, yawancin madaba'o'in da suka halarci nunin da aka shirya sun kafa dandalin musamman na nune-nune, inda suka yi kokarin gabatar da littattafai dangane da tarihi da al'adun gargajiyar kasar Sin. Kamar su littattafai dangane da wayewar kai da ba da ilmi , wato wani littafi dangane da halin kirki da aka bayyana ta hanyar yin amfani da kalmomi uku, da turanci ana kiransa "Three-Character Textbook for Beginesses or Primer Said", da Sinanci ana kiransa "Sanzijing" da littafin da ake kira "Mencius" da dai sauransu. Sa'anan kuma da akwai littattafai dangane da tarihin shahararrun mutane na zamanai aru aru na kasar Sin, mafiya yawansu su ne littattafai na kara ba da bayyani kan al'adun gargajiyar kasar Sin. Shugaban madaba'ar duniya ta yau Mr Song Zude ya bayyana cewa, yanzu, an fi kaunar al'adun gargajiya, bisa binciken da aka yi, an bayyana cewa, masu karantawa suna kara karuwa, kuma wadanda suke yin bincike kan al'adun gargajiya sai kara yawa suke yi, sa'anan kuma wadanda suke da sha'awar fanni su ma sai kara yawa suke yi. Kasar Sin tana da al'adun da ke da tarihi a shekaru fiye da 5000, ya zuwa yanzu da samun bunkasuwar zamantakewar al'umma, mutane suna kan waiwayon abubuwa na da, wannan ayyukan da ake yi ne a yau da kullum, a ganina, dawowar abubuwan gargajiya mafari ne da aka yi kawai.

Mr Zhu Liyong yana aiki a wata kafar yada labarai ta hanyar yin amfani da harsunan waje, bayan aiki, yana bincike kan al'adun gargajiyar kasar Sin, kuma yana da ra'ayinsa na kansa a fannin, ya bayyana cewa, na taba koyon harsunan waje, amma na ji cewa, ban fahimci al'adun kasar Sin ba. A cikin ma'amalar da na yi da mutanen kasashen waje, an taba nema na da na yi karin bayyani kan al'adun kasar Sin, duk saboda ni dan kasar Sin ne, amma ni kaina ban iya bayyana abubuwa da yawa dangane da al'adun kasar Sin ba. Ina dalilin da ya sa haka? Shi ne saboda da ban fahimci wadannan abubuwa a fannin ba, tun daga ranar da na soma karatu a makarantar firamare da ta sakandare da ta jami'a, abubuwa kadan ne nake samuwa daga wajen karatu, abubuwan da nake koyo yawancinsu daga kasashen yamma, saboda haka ya kamata mu soma binciken abubuwanmu na kanmu, wadanda ba mu mai da hankali sosai gare su a da ba.

1 2