Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-28 15:29:44    
Taron raya Afrika na Tokyo, ya gabatar da cewa, "Za a gina Afrika da ke da rayayyen karfi"

cri



Yaya za a taimaka wa kasashen Afrika don tabbatar da manufar samun bunkasuwa ta shekarar 2000 na M.D.D., shi ne kuma wani muhimmin batu na taron. Ciki kuwa abubuwan da suka fi muhimmanci su ne, bunkasa aikin ba da ilmi a kalla na firamare, da kyautata aikin kiwon lafiya. Yanzu Afrika na fuskantar kalubale mai tsanani a fannin bunkasa aikin ba da ilmi a kalla na firamare a dukkan fannoni, ba a iya samun isassun dakunan aji, da malamai, da kuma litattafan karatu. Bayan haka kuma, ko da ya ke Afrika ya samu wasu nasarori a fannin hana yaduwar ciwon sida, da ciwon kwalara, da kuma sauran ciwace-ciwace masu yaduwa, amma ya yi nisa don cimma manufar samun bunkasuwa ta shekarar 2000. Saboda haka, daga matsayin likitanci ya zama wani aikin da za a yi ba tare da bata lokaci ba.



A karkashin kokarin da kasashen duniya da Afrika kansa suka yi tare, a 'yan shekarun da suka wuce, rikice-rikicen siyasa da aka samu a yankin Afrika sun ragu kadan, kuma ana tsara tsarin hana da daidaita rikici, amma ko da ya ke haka, kullum rikice-rikicen siyasa su kan faru a yankin, ba kawai sun kawo hargitsin jin kai mai tsanani ba, har ma sun hana ayyukan tattalin arziki yadda ya kamata. Sabo da haka, taron zai ba da shawara kan kara bayar da taimako wajen aikin ba da ilmi, da kiwon lafiya, da sake tsugunar da 'yan gudun hijira, da kwace makamai, da dai sauransu.

Bayan haka kuma, a karo na farko za a shigar da matsalar sauye-sauyen yanayi cikin muhimman batutuwa na taron duniya game da raya Afrika na Tokyo. Dumamar yanayi ya kawo barazana sosai ga samun dauwamammen cigaba a Afrika, a waje daya kuma, za ta iya haifar da wasu ciwace-ciwace, a sakamakon haka, za a kara tsanantawar halin kiwon lafiya da Afrika ke ciki.


1 2