Tun daga ranar 28 zuwa ranar 30 ga wata a birnin Yokohama, birnin da ke bakin teku a kasar Japan, za a shirya taron duniya game da raya Afrika a Tokyo a karo na hudu, manyan shugabannin gwamnatoci, da manyan wakilai daga Afrika, da wasu kasashen Asiya da yawansu ya kai fiye da 1000 za su halarci taron. Babban batu na taron shi ne "Gina Afrika da ke da rayayyen karfi: wani babban yankin da ke cike da fata da dama".
A kan shirya taron duniya game da raya Afrika a Tokyo a ko wane shekaru biyar. Muhimman batutuwa na taron, sun hada da: tattauna da tsara shirin bunkasa gine-ginen manyan ayyuka na Afrika, da taimaka wa Afrika wajen tabbatar da manufar samun bunkasuwa ta shekarar 2000 ta M.D.D. ta hanyar bunkasa aikin ba da ilmi a kalla na firamare, da kiwon lafiya, da kuma bayar da taimako ga kasashen Afrika wajen magance sauye-sauyen yanayi, da dai sauransu.
Akwai mutanen da yawansu ya wuce miliyan 900 a babban yankin Afrika, kuma yana da arzikin albarkatun kasa, yana da boyayen karfi sosai wajen samun bunkasuwa. Amma, rasa cikakkun manyan ayyuka, da jarin waje, da kuma sauran dalilai, sun hana bunkasuwar tattalin arziki na Afrika.
A gun taron, za a tattauna kan yaya za a sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki na Afrika, da kuma samun dauwamammen cigaba a fannin tattalin arziki a Afrika, ta hanyar bunkasa manyan gine-gine da farko, da kyautata muhallin Afrika don jawo jarin waje, da kuma kara bayar da kudi kan sha'anin noma, don karfafa karfin kawo albarka.
Aikin gine-ginen muhimman ayyukan kasa, inji ne na bunkasuwar tattalin arziki a Afrika. A gun taron, za a mayar da hankali kan tattauna da tsara shirin bunkasa manyan ayyukan kasa a Afrika, ciki har da gina zirga-zirgar hanyoyin mota bisa matsayi daban daban, da tashoshin ruwa, da tashoshin samar da wutar lantarki, da dai sauransu, don neman bunkasuwar tattalin arziki, ta yadda za a kawo bunkasuwar sha'anin noma, da masana'antu.
1 2
|