Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-26 19:32:07    
Kasar Sin ta dauki matakai don maganin aukuwar matsaloli a sakamakon girgizar kasa

cri

Yanzu, aikin shawo kan bala'in girgizar kasa da kasar Sin take yi yana nan yana ci gaba cikin gaggawa. Cikin himma da kwazo ne aka zaunar da mutanen da suka gamu da bala'in girgizar kasa da kuma sake gina gidajen kwana da farfado da tattalin arziki, a sa'I daya kuma, yadda za a yi rigakafin sake faruwar matsaloli a sakamakon bala'in girgizar kasa, musamma ma sake faruwar barna saboda ayyukan ruwa da tafkokin da aka samu saboda duwatsun da  suka gangara suka katse ruwan kogi , wannan ya riga ya zama abu mai muhimmanci da ya jawo hankulan rukunoni daban daban. A gun taron ganawa da manema labaru da Majalisar gudanrwa ta kasar Sin ta shirya a ranar 25 ga wannan wata, wani jami'in da abin ya shafa ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta tsai da shirin ko ta kwana a kan ayyukan ruwa da tafkokin da aka samu saboda duwatsun da suka gangara zuwa kasa suka katse ruwan kogi, da kuma tsara shirin kawar da hadarurruka da kaurar da jama'a. Ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta don rage matsalolin da za su auku a sakamakon bala'in girgizar kasar da kuma bada tabbaci ga kare rayuka da dukiyoyi na jama'a.

Matsalolin da za su faru a sakamakon girgizar kasa su ne sauran matsalolin daga indallahi da suka faru a jere a sakamakon girgizar kasa. Alal misali, bala'in girgizar kasa zai iya haddasa annoba, kuma zai iya lalata matsadar ruwa, har zai haddasa bala'in ambaliyar ruwa a sakamakon lalatacciyar madatsar ruwa, ko bututun masana'antun harhada magunguna suna katsewa ta yadda iska mai dafi yana iya  fita ya gurbata muhalli da sauransu. Bayan aukuwar lamarin girgizar kasa a lardin Sichuan na kasar Sin a wannan gami, kasar Sin ta kara karfi ga ayyukan kiwon lafiya na yin rigakafin annoba , kuma an kawar da wadanda suke gurbatar da wurare, a daidai lokacin ne aka kawar da bala'in muhalli da zai auku . Ya zuwa yanzu, ba a sami lamarin aukuwar annoba a wuraren da suka gamu da bala'in girgizar kasa ba, amma girgizar kasa ya sa wasu madatsar ruwa sun lalace, kuma tafkokin da aka samu a sakamakon girgizar kasa suna kawo kalubale mai tsanani ga wuraren da ke karshen yankunan kogin.

A gun taron ganawa da manema labaru da aka yi a ranar 25 ga wannan wata, mataimakin ministan ayyukan ruwa Mr E Jingping ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 25 ga wannan wata da karfe 8 da safe, an riga an sami tafkokin da yawansu ya kai dubu 2 ko fiye a sakamakon girgizar kasa, ya ce, ma'aikatar ta mai da hankali sosai a kan wadannan ayyukan ruwa da tafkoki. Ya bayyana cewa, game da matarin ruwa da suka riga suka sami hadarin lalacewa, ma'aikatar ayyukan ruwa ta riga ta shirya kwararru don yin bincike a kansu, wasu an rage ruwan da ke cikinsu, wasu kuma an riga an zubar da dukkan ruwan da ke cikinsu.

Mr E Jingping ya bayyana cewa, ma'aikatar ayyukan ruwa ta kuma shirya kwararru da kungiyoyin ba da ceton agaji don kara inganta wadannan ayyukan da suka riga suka sami cikas.

1 2