Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-26 19:19:12    
Ana kokarin kiyaye yanayin kasa a jihar Hainan ta kasar Sin

cri

Sana'ar yawon shakatawa muhimmin ginshiki ne ga kiyaye yanayin kasa a jihar Hainan. Malam Zhang Qi, babban direktan hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta jihar yana ganin cewa, kiyaye yanayin kasa yana da muhimmanci sosai ga bunkasuwar harkokin yawon shakatawa a jihar Hainan. Ya kara da cewa, "kiyaye yanayin kasa tushe ne da ake dogara don ciyar da sana'ar yawon shakatawa zuwa babban matsayi a jihar Hainan, kuma yana da muhimmanci sosai ga kara jawo masu yawon shakatawa daga kasashen waje. Yawon shakatawa a dazuzzuka na wuri mai zafi da tekuna da wuraren marmaro da makamantansu yawon shakatawa ne da ake yi ba tare da gurbata muhalli ba, don haka muna kokarin raya su a jiharmu. Wa zai yi yawon shakatawa a bakin teku da aka gurbata shi? Sabo da haka muna iyakacin kokari wajen kiyaye yanayin kasa a jiharmu."

Yanzu kiyaye muhalli ya riga ya zama ra'ayi daya da bangarori daban daban na jihar Hainan suka samu. Daga kasafin da hukumar jihar Hainan ta tsara, an gano cewa, jihar za ta ci gaba da yin kokari wajen kiyaye yanayin kasa da dashe-dashen itatuwa da kara zuba kudade masu yawa wajen kiyaye muhalli da sauransu. (Halilu)


1 2