Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-26 19:19:12    
Ana kokarin kiyaye yanayin kasa a jihar Hainan ta kasar Sin

cri

A shekarar 1999, jihar Hainan ta kasance sahon gaba wajen kiyaye yanayin kasa a Sin. Bayan haka a shekarar bara, jihar ta sake tsara manyan tsare-tsaren kiyaye yanayin kasa. Da Malam Zhu Yunshan, mataimakin babban direktan hukumar kula da harkokin bunkasuwa da kwaskwarima ta jihar ya tabo magana a kan wannan, sai ya bayyana cewa, kiyaye yanayin kasa da kyau yana da muhimmanci sosai ga samun bunkasuwa mai dorewa a jihar Hainan. Ya kara da cewa, "hukumar jihar ta fahimci cewa, dole ne, a kiyaye yanayin kasa a jihar Hainan da kyau. Wannan babban bukatun ne da ake yi don samun bunkasuwa mai dorewa a jihar. Yayin da ake bunkasa masana'antu a jihar, a bukaci masana'antun da su samar da kayayyaki ba tare da gurbata muhalli ba. Manyan ka'idoji uku da ake bi wajen bunkasa aikin masana'antu su ne, ba a gurbata muhalli, ba a lalata albarkatun kasa, kuma ba a maimaita yin ayyuka da ba na zamani ba. "

Bayan haka Malam Zhu Yunshan ya ci gaba da cewa, ko da yaushe hukumomin matakai daban daban na jihar suna mai da hankali sosai ga ayyukan da ake shigo da su daga sauran wurare, ta yadda za a shigo da manyan masana'antu da manyan ayyukan wadanda ke da kyawawan kayayyakin aiki da sauke da nauyi bisa wuyansu na zamantakewar al'umma, kuma ba su gurbata muhalli.

Tun daga shekarar 2005, hukumar jihar Hainan ta fara kokari sosai wajen kiyaye yanayin kasa ta hanyar kafa dokoki da tsara fasali da zuba jari da sauransu.

Jihar Hainan ta dauki aikin noman kayayyakin gona iri na wuri mai zafi a matsayin manyan tsare-tsarenta. Ta yi kokari sosai don yadada hanyar zamani da ake bi wajen yin aikin noma ba tare da gurbata muhalli ba. Malam Yang Sitao, shugaban gunduma mai suna Chengmai ta jihar wadda take daya daga cikin manyan gundumomin aikin noma 10 na kasar Sin ya bayyana cewa, "jami'an jihar Hainan da jama'arta dukanninsu suna mai da hankali sosai ga kiyaye yanayin kasa. Idan an so a kiyaye yanayin kasa da kyau a jihar, to, wajibi ne, ko da yaushe a sa aikin kiyaye yanayin kasa a gaban kome, a lokacin da ake yin dukkan ayyuka wadanda suka hada da aikin noma. Jihar Hainan ta fara kiyaye yanayin kasa a fannin aikin noma tun da wuri. Ana samun tsire-tsire a dukan shekara a jihar, don haka ana samun takin Allah cikin sauki. Hukumar jihar ta yi kokari sosai wajen gina ramukan tarin shara don samar da gas ga manoma, sa'an nan ana samun takin Allah mai yawa, yanzu manoman jihar Hainan wadanda ke samun gas daga tarin shara sun yi yawa idan an kwatanta su da na sauran jihohi a kasar Sin. "

1 2