Yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu ci gaba da gabatar muku da wannan bayani kan cewa, shan kofi da yin hutu kadan za su iya taimaka wa direbobi wajen kara mai da hankali yayin da suke tuka mota da dare.
Sakamakon binciken ya bayyana cewa, game da mutane masu aikin sa kai da suka sha kofi da kuma yin hutu a kan hanya, kashi 75 da kuma kashi 66 bisa kashi dari daga cikinsu bi da bi ne suke da hali iri guda rana da dare, wato sau daya ne kawai da suka karya ka'idojin zirga-zirga. Amma game da mutanen da suka sha kofin da ba shi da sinadarin caffein a ciki ba, kashi 13 bisa dari daga cikinsu ne kawai suke da hali iri guda rana da dare, sauran mutane kuma sun karya ka'idojin sau da yawa har ma wani ya zarce sau 17.
Kwararru na kasar Faransa sun nuna cewa, a lokacin da, mutane su kan dora muhimmanci a kan illar da tuka mota bayan shan giya ke haihuwa kawai, amma ba su kula da illar da tuka mota yayin da ake ji gajiya ke haihuwa ba. A hakika dai, hadarurukan mota masu tsanani da yawansu ya kai kusan kashi 30 cikin dari sun faru ne sabo da jin gajiyar tuka mota. Amma sun yi gargadin cewa, ko shan kofi ko yin hutu cikin gajeren lokaci suna iya tabbatar da direbobi da su kara mai da hankali a cikin awoyi hudu ne kawai, sabo da haka dole ne a yi hutu sau da yawa lokacin da ake tuka mota cikin dogon lokaci.(Kande Gao) 1 2
|