Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 15:14:07    
Shan kofi da yin hutu kadan za su iya taimaka wa direbobi wajen kara mai da hankali yayin da suke tuka mota da dare

cri

A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan cewa, shan kofi da yin hutu kadan za su iya taimaka wa direbobi wajen kara mai da hankali yayin da suke tuka mota da dare.

Bisa sakamakon wani sabon binciken da kasar Faransa ta yi, an ce, a bayyane ne shan kofi ko yin hutu cikin gajeren lokaci za su iya taimaka wa direbobi wajen kara mai da hankali yayin da suke tuka mota da dare, ta haka za a iya rage yawan hadarin mota.

Ma'aikatar kula da zirga-zirga ta kasar Faransa ta dora muhimmanci sosai kan wannan sakamakon binciken da furofesa Philips da sauran manazarta na asibitin da ke karkashin jagorancin jami'ar Bordeaux ta kasar suka samu. Kuma ta tsai da kudurin cewa, daga ran 11 ga watan Yuli na shekara ta 2007, an fara yin furofaganda kan abubuwan da ya kamata direbobi su mai da hankali a kai yayin da suke tuka mota da dare a duk fadin kasar ta talibijin da rediyo, ta yadda jama'a za su iya magance matsalar tuka mota yayin da suke jin gajiya.

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Faransa suka bayar, an ce, manazarta sun zabi mutane masu sa kai 12 da ke da lafiyar jiki domin su tuka motoci har kilomita 200 daga karfe 2 zuwa karfe 3 da rabi da sassafe. Dukkansu sun shiga gwaji har sau uku, kuma tsawon lokacin da ke tsakanin ko wane gwaji ya kai makwanni da dama. Kafin an yi gwaji na farko, mutane masu sa kai sun sha kofin da ba shi da sinadarin caffein a ciki ba. A karo na biyu sun sha kofin da ke da sinadarin caffein miligram 200 a ciki, a karo na uku kuma sun yi hutu har mintoci 30 a gefen hanya lokacin da suke tuka mota. A karshe dai ko wanensu ya tuka mota daga karfe 5 zuwa karfe 6 da rabi da yamma domin yin kwantata da halin da suke ciki yayin da suke tuka mota da dare.


1 2