Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 15:12:23    
Masana'atun yin kayayyakin al'adu da ke kara samun bunkasuwa da saurin gaske a birnin Beijing

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, birnin Beijing ya yi kokarin raya masana'antun yin kayayyakin al'adu, sa'anan kuma ya mayar da ra'ayin da ke cewar "wasannin Olimpic sun dace da al'adun 'Yan adam" don zama daya daga cikin manufofin shirya wasannin Olimpic na shekarar 2008 a birnin Beijing. Bisa halin nan ne, yankin fasahohi mai lamba 798 ya sami bunkasuwa da saurin gaske. Mr Chen Yongli ya bayyana cewa, a karshen shekarar 2005, birnin Beijing ya gabatar da shawarar mai da muhimmanci ga raya masana'antun yin kayayyakin al'adu. A wancan lokaci, da yake yankin fasaha mai lamba 798 ya sami bunkasuwa da saurin gaske, kuma ya yi suna sosai a kasa da kasa, bayan binciken da shugabannin da abin ya shafa suka yi, ana ganin cewa, yankin fasaha mai lambar 798 ya riga ya shiga lokacin da yake bukatar samun jagorancin bunkasuwa wajen tsara fasalinsa, kuma abu mafi kyau shi ne zai iya zama wani muhimmin wuri mai daraja na birnin Beijing . A shekarar 2006, aka mayar da yankin da ya zama yankin da masana'antun yin kayayyakin al'adu suke zama a cunkushe.

Yanzu, a yankin, wasu shahararrun masana'antun yin kayayyakin al'adu suna nan a cunkushe. Ya zuwa watan Yuli na shekarar 2007, yawansu ya kai 354, wadanda suka hada da dakunan yin zane-zane da ofishoshin aiki na mutane masu zaman kansu da rumfunan daukar sinima da ayyukan daukar wakoki da shirye-shiryen TV da sauransu. An ce, yankin ya iya tsayawa kan matsayin da ya yi daidai da wani shahararren yankin fasaha na birnin New York na kasar Amurka. Malama Chen Linghui da ta zo daga Taiwan ta bayyana cewa, a shekarar 1994, na taba zuwa birnin Beijing don kai ziyarar yi wa malamina bakunci , a wancan lokaci, na yi tsammanin kafa dakin fasaha nawa a birnin Shanghai, amma bayan da na kai ziyara a yankin fasaha mai lamba 798, sai na yi mamaki sosai, na yi bakin ciki da makarata ta zuwa yankin , kai , wurin nan ya yi kama da wurin fasaha na Soho na birnin New York. Yanki mai lamba 798 shi ne wani sansanin yin kayayyakin al'adu na birnin Beijing. Wasu wuraren birnin Beijing da suka yi kama da yankin mai lamba 798 sun hada da kauyen Son da Huajiadi , wadanda darurukan masu yin zane-zane suke aiki a ciki, a yankin Shijingshan na birnin Beijing, ana nan ana kafa sansanin yin kayayyakin Cartoon da wurin ni'shadi da sauransu, birnin Beijing ya kuma kafa kungiyar ba da shugabanci ga masana'antun yin kayayyakin al'adu, sa'anan kuma ya ware kudaden da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 500 don ba da goyon baya ga ayyukan raya kayayyakin al'adu.

Ba shakka a shirya ya ke, birnin Beijing zai kafa wuraren da suke iya samun masana'antun yin kayayyakin al'adu 30.(Halima)


1 2