Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 15:12:23    
Masana'atun yin kayayyakin al'adu da ke kara samun bunkasuwa da saurin gaske a birnin Beijing

cri

Idan kai mai kaunar fasaha ne, kuma za ka kai ziyara a birnin Beijing, to , bai kamata ba ka rasa ziyara zuwa wani yankin fasaha na 798, inda darurukan masu fasahohi suke taruwa gu daya tare da zane-zane da mutum mutumai da hotuna da dai sauransu, wato masu fasaha sun nuna kwarewa sosai a fannoni iri iri. Wurin ya riga ya zama daya daga cikin muhimman sansanonin masana'antun yin kayayyakin al'adu na birnin Beijing.

Yankin fasaha na 798 yana nan dab da filin jiragen sama na kasa da kasa na birnin Beijing. A da, wurin shi ne ma'aikatar yin kayayyakin lantarki. A shekaru 90 na karnin da ya shige, ma'aikatar ta yi kwaskwarima, kuma ta canja ayyukanta tana yin sauran ayyuka, saboda haka dakunan ma'aikatar na da yawa wadanda ba a yi amfani da su ba. Wani direktan ofishin kula da harkokin yankin Mr Chen Yongli ya bayyana cewa, bisa wata damar da aka samu kwatsam ne, aka mayar da tsoffin masana'antun tarihi da su yi nasaba da fasahohi, kuma suka sami sabuwar damar rayuwa. Mr Chen Yongli ya bayyana cewa, yankin ya yi nasaba da fasahohi a hukunce ne a shekarar 1996, a wancan lokaci, lokacin ya yi daidai da ranar cika shekaru 60 da yin yakin kin harin Japan. A lokacin, wanda ke aiki a jami'ar koyar ilmin fasaha ta tsakiya ta kasar Sin Mr Sui Jianguo ya karbi wata dawainiya ta shirya nunin rukunan mutum mutumai da aka sassaka a jikin duwatsu dangane da jarumai masu yin dagiya da harin Japan. Don neman wani wurin da za a iya ajiye manyan rukunan mutum mutumai da aka sassaka a jikin duwatsu, sai aka zabi ma'aikata mai lamba 798. A lokacin farko, an yi hayar dakuna masu murraba'in mita dubu 3, sa'anan kuma sauran mutane su ma sun tafi wurin don haya sauran dakuna don yin aikin fasaha. Kai, an yada labarin daga nan zuwa can, sa'anan kuma masu fasahohi da yawa suna zuwa wurin don yin aikinsu na fasahohi.


1 2