Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-16 18:02:38    
Wani mai daukar hotunan naman daji na kasar Sin mai suna Xi Zhinong

cri

 

Mr Xi Zhinong ya bayyana cewa, kasar Sin tana daya daga cikin kasashen duniya da aka dauki hotunan naman daji da wuya, a daji, ana karancin manyan naman daji, kuma naman daji suna jin tsoron mutane sosai, amma, ya yi nasarar daukar hotunansu ta hanyar yin amfani da camara da sauran injuna.

Hoton da ya dauka na biri mai gashin launin zinariya ya iya wakiltar dukkan hotunan da ya dauka. Biri mai gashin launin zinariya yana zaman rayuwa a manyan tsaunuka masu sanyi sosai da ke tsakanin lardin Yunan da jihar Tibet na kasar Sin, irin biri tsirari ne da kasar Sin take da shi. Yanzu yawansu ya kai 1500 ko fiye.

Bisa matsayinsa na musamman na mai daukar hotunan naman daji, Mr Xi Zhinong yana fatan kowa ya mai da hankali ga kiyaye muhalli. Ya bayyana cewa, a da, na taba fatan koyon ilmin daukar hotunan tsuntsaye wadanda na fi kaunarsu ta hanyar yin amfani da camara, amma yanzu, na kara kaunar tsuntsaye ta hanyar daukar hotunansu. Yanzu muhallinmu ya lalace sosai da sosai, a wani fanni, ya kamata gwamnati ta mai da hankali ga shawo kan batun, a wani fanni daban kuma,ya kamata kowa ya mai da hankali ga kiyaye muhallinmu, abin faranta ran mutane shi ne, samari sai kara yawa suke yi suna shiga aikin kiyaye muhallinmu.

Ta hanyar ayyukan kiyaye halittu da muhallinmu, Mr Xi Zhinong ya ji cewa, dukkan zamantakewar al'umma suna kara daga matsayin tunaninsu na kiyaye muhalli, ya bayyana cewa, na yi farin ciki da ganin cewa, samari sai kara yawa suke yi sun mai da hankali ga ayyukan kiyaye halittu da muhallinmu. Idan kowa ya shiga aikin, to ko shakka babu muhallin kasar Sin zai iya samun kyautatuwa.

A cikin hotunan da Mr Xi Zhinong ya dauka, duniyar naman daji na da wadatuwa da kyaun gani sosai, kuma wadannan naman daji sun yi tamkar yadda suke da hazikanci sosai, kuma suke yin magana da mutane cikin jituwa.(Halima)


1 2