Mr Xi Zhinong shi ne mai daukar hotunan namun daji da ke cikin masu daukar hotunan namun daji marasa yawa na kasar Sin. A watan Augusta na shekarar 2003, a gun bikin nuna sinimar namun daji na kasa da kasa na kasar Japan da aka shirya a birnin Fukuyama na Japan , hoton da Mr Xi Zhinong ya dauka da ke da lakabi haka "ana bin sawun biri mai gashin launin zinariya na lardin Yunan na kasar Sin" ya sami lambar yabo na sinima mafi kyau na kasashen Asiya, kuma shi ne mai samun lambar yabo na koli na kasar Sin wajen aikin kiyaye muhalli, wato lambar yabo ta duniya.
Mr Xi Zhinong da ke da shekaru 44 da haihuwa shi ne mai dogo tare da jan fuska bisa sakamakon hasken rana a fadadan manyan tsaunuka, yana murmushi a yau da kullum tare da nuna jin tausayi, ya taba aiki a gidan TV na tsakiya na kasar Sin wato gidan CCTV na kasar Sin. A shekarar 1998, ya bari aikinsa a gidan TV, ya zama mai daukar hotuna cikin 'yanci kuma mai sa kai ga kiyaye muhalli. Ya tanada hotunan zaman rayuwar naman daji ta hanyar yin amfani da camara . Mr Xi Zhinong ya ce, zaman rayuwar da ya zaba na daukar hotunan naman daji na da nasaba da zaman rayuwarsa na lokacin yarantaka. Ya bayyana cewa, a lokacin da nake karami, na yi zaman rayuwa a wani wuri mai ni'ima, saboda haka, na taba kiwon agwagi da tsuntsaye, har ma na taba kama kifaye don kiwon agwagi, a gaskiya dai na kusanci halittu sosai, alal misali, a daren, na kan ji kukan mujiya, duk saboda a makarantarmu, da akwai wasu mujiyoyin da suke zama a kan bishiya, wani lokaci ma, na taba jin kukan kura a wurin waje da makarantarmu.
Garin Mr Xi Zhinong yana gundumar Wei da ke yankin Dali na kabilar Bai mai ikon aiwatar da harkokinsa na kansa na lardin Yunan na kasar Sin, inda ana iya ganin bishiyoyi da tsire-tsire masu kore shar a ko'ina tare da naman daji da yawa. A lokacin da ya cika shekaru goma, ya tafi birnin Kunming mai wadata tare da iyayensa, da ya bari karamin birnin da ke da halin kauyuka, sai ya ji cewa, birnin bai dace shi ba, amma bai yi tsammani cewa, bayan shekaru 20 da suka wuce, ya koma wurin da ya san shi sosai da sosai, wato garinsa ke nan, kuma ya yi aikin musamman na daukar hotunan naman daji, daga nan sai zaman rayuwarsa ya kara kyau sosai.
1 2
|