Wajen samar da magunguna da ake yi da abubuwa masu rai kuma, ksar Afirka ta kudu ta shimfida masana'antun kera magunguna da ke dogara ga fasahohin halittu na zamani na uku, haka kuma kasar Afirka ta kudu ta zama matsayi kafin goma a duk duniya wajen kera magunguna, da kera maganin kashe kwari ta hanyar yin amfani da tsire. Ban da wannan kuma, hukumomin likitanci ta kasar Afirka suna mai da hankali sosai kan nazarin yadda ake yin rigakafi da warkar sababbin cututtukan da suka fito ba da dadewa ba.
A halin yanzu dai, manufofi da kuma matakai da kasar Afirka ta kudu ta dauka wajen kare abubuwa masu rai iri daban daban su ne, kaddamar da babban shirin nazarin fasahohin halittu bisa kere kere, da sa kaimi ga nazari kan sababbin magunguna da fasahohin gene da dai sauransu, da kaddamar da babban shirin nazarin fasahohin halittu na aikin gona da shirin kere kere, wanda ake fi mai da hankali ne kan canzawar kwayoyin halitta.(Danladi) 1 2
|