Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta zuba jari da yawa, da kuma sa kaimi ga yin kere kere a fannonin tsire tsir????e na canzawar kwayoyin halitta wato 'gene', da makamsahi da aka samu ta hanyar yin amfani da tsire, da kuma magunguna da ake yi da abubuwa masu rai, da kare abubuwa masu rai iri daban daban, sabo da haka ne, ya samu kyawawan nasarori wajen nazarin fasahohin halittu, ta yadda za ta kago sharudda masu kyau wajen yin amfani da fasahohin halittu a fannin aikin gona.
Kasar Afirka ta kudu ta samu saurin bunkasuwar sha'anin tsire tsire na canzawar kwayoyin halitta wato 'gene'. Kasar Afirka ta kudu ta zama wata kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta yarda da shigar da tsire tsire na canzawar kwayoyin halitta, da kuma shuka su bisa makasudin kasuwanci.
Bi da bi ne, kasar Afirka ta kudu ta kaddamar da dokar abubuwan halittu, da manyan tsare tsare na kasar Afirka ta kudu wajen nazarin fasahohin halittu, da kuma shirin sa kaimi ga jama'a da su fahimci fasahohin halittu, da kuma dokar kare abubuwa masu rai iri daban daban. A sa'i daya kuma, kasar Afirka ta kudu ta gaggauta hada kanta da sauran kasashen da ke kudancin nahiyar Afirka, domin sa kaimi ga hada kansu wajen amfani da fasahohin halittu a wannan yanki.
Domin kara sa kaimi ga nazari da kuma yin amfani da makamashi da aka samu ta hanyar yin amfani da tsire, da kuma rage matsi daga bukatar man fetur, da kuma kara biyan bukatar kare muhalli da kara ayyukan yi ga jama'a, ma'aikatar makamashin ma'adinai ta kasar Afirka ta kudu ta fito da manyan tsare tsare na masana'antun makamashi da aka samu ta hanyar yin amfani da tsire, ta yadda za a ba da jagora sosai ga bunkasuwar sha'anin samun makamashi ta hanyar yin amfani da tsire.
1 2
|